Tuesday, February 17
Shadow

Duk Labarai

T-Pain na nufin wahala ta karamin lokaci, Tinubu zai sake cin zabe a 2027>>Inji Doyin Okupe

T-Pain na nufin wahala ta karamin lokaci, Tinubu zai sake cin zabe a 2027>>Inji Doyin Okupe

Duk Labarai
Tsohon kakakin shugaban kasa, Doyin Okupe ya bayyana cewa, 'yan Najeriya zasu sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa dan ya kammala shekaru 8 kamar ya da doka ta bashi dama. Okupe ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels. Yace idan Tinubu ya magance matsalar wutar lantarki sannan ya maganace matsalar man fetur sannan ya magance matsalar abinci to 'yan Najeriya da kansu zasu fito au ce sai shine suke so ya ci gaba da mulki a shekarar 2027. Yace kuma sunan T-Pain da ake gayawa Tinubu yana nufin wahala ce ta dan lokaci wadda nan gaba zata zama abin Alheri.
Ban fadi zabeba, Magudi aka yi, Abin dariyane ka rasa abinda zaka yi akan wahalar da ka saka mutane a ciki saidai kace a yi addu’a>>Atiku ya mayarwa Tinubu Martani

Ban fadi zabeba, Magudi aka yi, Abin dariyane ka rasa abinda zaka yi akan wahalar da ka saka mutane a ciki saidai kace a yi addu’a>>Atiku ya mayarwa Tinubu Martani

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP,Alhaji Atiku Abubakar ya mayarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu martani kan maganar da ya masa ta cewa tsare-tsaren shi da yake baiwa Tinubu shawarar ya dauka ba'a gwadasu an ga yanda suke aiki ba. Atiku yace gaggawa wajan daukar matakai ba tare da taka tsantsan ba ne da gwamnatin 'yan koyo ta Tinubu ke yi ne ya jefa kasarnan cikin wahala. Atiku yace abin mamaki ne ace bayan da ya yi kiran a kawo gyara,Tinubu ya rasa irin gyaran da zai kawo saidai yace a yi addu'a....
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa dòn tayi kira kan mátsalar tsaròɲ garinsu

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa dòn tayi kira kan mátsalar tsaròɲ garinsu

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa don tayi kira ga Gwamnan jihar kan halin rashin tsaron da ya addabi garinsu a wani bidiyon da ya yita yawo na budurwar a kafofin sada zumunta inda budurwar take kiran sunan Gwamnan kai tsaye akan lamarin rashin tsaro. Abba Pantami ya samu sahihin labarin cewa a jiya Lahadi Gwamnatin jihar ta tura aka kama budurwar inda a yau Litinin ta gabatar da ita a gaban kotu kan zargin yiwa Gwamnan jihar rashin kunya. A yanzu haka budurwar tana tsare a hannun hukuma a jihar Sokoto, sunan budurwar Hamdiya Sidi dake karamar hukumar Wurno jihar Sokoto, garin nasu yana daya daga cikin yankunan dake fama da matsalolin rashin tsaro. Daga Shafin Dokin Karfe TV
An yiwa malamin Islamiya Daurin rai da rai bayan da yawa dalibarsa me shekaru 14 fyade a Masallaci

An yiwa malamin Islamiya Daurin rai da rai bayan da yawa dalibarsa me shekaru 14 fyade a Masallaci

Duk Labarai
Kotun dake kula da cin zarafin mata da rikicin cikin gida dake Ikeja jihar Legas ta yiwa wani malamin Islamiya daurin rai da rai bayan samunsa da laifin yiwa dalibarsa me shekaru fyade. Malamin me suna Alani Rafiu ya kai yarinyar masallaci inda ya mata fyade kuma ba sau daya ba sannan ya bata kudi dan kada ta gayawa kowa. Mai Shari'a, Justice Rahman Oshodi ya bayyana cewa, malamin ya ci amanar iyayen yarinyar da suka amince dashi suka kaita wajanshi dan ya koyar da ita. Sannan ya bata mata rayuwa a lokacin da ya kamata ace hankalinta na kan karatune. Dan haka ya yanke masa daurin rai da rai sannan yace za'a saka sunansa a cikin rijistar masu fyade na jihar.
A jihar Borno ma an gurfanar da kananan yara a gaban kotu bisa zargin shiga Zanga-zanga da batawa gwamna Zulum Suna

A jihar Borno ma an gurfanar da kananan yara a gaban kotu bisa zargin shiga Zanga-zanga da batawa gwamna Zulum Suna

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Borno na cewa a can ma an gurfanar da kananan yara a kotu bisa zargin shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da daga tutar Rasha. Wadanda aka gabatar din su 19 ne wanda cikinsu akwai guda 3 wanda kananan yara ne. Wannan na zuwane bayan da aka yi shigen irin hakan a babban birnin tarayya, Abuja. Mai Shari'a, Justice Aisha Mohammed Ali ce ta jagoranci zaman kotun kuma kananan yaran da aka gabatar a gabanta suna da shekaru 14 ne zuwa 15. Babbar Lauya a jihar ta Borno, Hauwa Abubakar ce ta gabatar da karan inda ta zargi wadanda aka gurfanar da batawa Gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum suna da kuma tunzura mutane su yiwa gwamnati bore da kuma shirin daukar makamai. Hakanan wasu daga cikinsu an zargesu da daga tutar Rasha. Duka dai sun musanta zargin da ake musu...
Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan Tituna a duk fadin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan Tituna a duk fadin Najeriya

Duk Labarai
A shirye-shiryen bukukuwan karshen shekara, Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan titunan kasarnan. Hukumar dake kula da titunan Najeriya, FERMA ce dai ta ke kula da gyaran. Shugaban hukumar, Engr. Chukwuemeka Agbasi ne ya kaddamar da fara gyaran titunan a jihar Kano. Yace za'a yi wadannan kyaran ne dan samarwa mutane saukin ziyara da komawa garuruwansu dan yin bukukuwan karshen shekara. Yace sun gano titunan da aka fi amfani dasu kuma sune zasu fi baiwa fifiko a wajan gyaran. Ya bayyana cewa, wannan aiki zai samarwa da mutane akalla 12,000 abin yi wanda hakan zai habaka tattalin arzikin kasa.
Ku daina Tsinuwa da zagi ga shuwagabanni, Addu’a ya kamata ku rika musu>>Sarkin Musulmi ga ‘yan Najeriya

Ku daina Tsinuwa da zagi ga shuwagabanni, Addu’a ya kamata ku rika musu>>Sarkin Musulmi ga ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Me Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na II ya yi kira ga 'yan Najeriya su daina tsinewa da kuma la'antar shuwagabanni inda yace su mayar da komai ga Allah. Yace 'yan kasa su rika yiwa shuwagabanni addu'a da ma kasar baki daya. Yace babu wani abu me kyau ko marar kyau dake dawwama,koma menene zai wuce kamar ba'a yi ba. Ya kuma jawo hankalin shuwagabanni dasu san cewa zasu tsaya a gaban Allah dan amsa yanda suka gudanar da mulki inda babu wanda zai karesu. Sannan yayi kira ga malamai da su rika gayawa mabiyansu gaskiya. Sarkin yayi wannan jawabine a wajan wani taro da ya gudana a Kaduna ranar Litinin inda aka hada malaman Addinin Musulunci da Kiristanci.
EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Delta kuma mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023, Efeanyi Okowa kan almundahanar Naira Tiriliyan 1.3

EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Delta kuma mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023, Efeanyi Okowa kan almundahanar Naira Tiriliyan 1.3

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta kasa,EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Delta,Efeanyi Okowa akan zargin Almundahanar kudi. Ana zargin tsohon gwamnan da karkatar da Naira Tiriliyan 1.3. Kudin dai an bayyanasu a matsayin kaso 13 dinnan da ake warewa jihohin da ake hako man fetur a cikinsu. Wata majiya data san da lamarin tace an karkatar da kudadenne a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023. An kama Okowa ne a ranar Litinin a Birnin Fatakwal na jihar Rivers a yayin da ya je ofishin EFCC amsa gayyatar da suka masa. Hakanan ana kuma zargin tsohon gwamnan da karkatar da wasu kudaden na daban da suka kai Naira Biliyan 40

Tinubu Ya Himmatu Wajen Rage Raɗaɗin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki, Inji Minista

Duk Labarai
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar rage raɗaɗin da ‘yan Nijeriya ke ciki. Idris ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Kaduna a shirin ‘Hannu Da Yawa’ na Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Sashen Hausa. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa ministan ya yi magana kan wahalar da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, kuma ya ce tallafin yana amfanar wasu tsirarun mutane ne kawai. Ya ba da tabbacin cewa tattalin arzikin ƙasar nan zai daidaita, kuma babu wata gwamnati da za ta so a samu ci-baya a zamanin ta. Idris ya jaddada cewa abin da ya kamata a gyara a ƙasar nan ba ya ta’allaƙa ne ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wakilai da aka zaɓa ko kuma masu zartaswa na gwamnati kawai ba ne, ...