Monday, February 16
Shadow

Duk Labarai

Shugaba Tinubu Ya Tallafawa Ma’aikata Da Ɗalibai Da Gudummawar Motocin Sufuri

Shugaba Tinubu Ya Tallafawa Ma’aikata Da Ɗalibai Da Gudummawar Motocin Sufuri

Duk Labarai
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cika alƙawarin da yayi na ba da kyautar motoci ga ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai domin sauƙaƙa musu harkokin sufuri. An ƙaddamar da ba da motocin yau a fadar shugaba ƙasa, Abuja inda aka miƙa motocin bas-bas guda (64) masu amfani da iskar gas ta (CNG) ga shugabancin ƙungiyoyin. Idan ba a manta ba, tun bayan cire tallafin man fetur ne dai shugaban ƙasar yayi alƙawarin tallafa wa ma'aikata da ɗalibai da motocin sufuri masu amfani da iskar Gas waɗanda za su rage musu kashe kuɗaɗe wajen zirga-zirgarsu ta yau da kullum.
JARABTA: Cikin Kwanaki Uku A Jere, Ya Rasa Matarsa Da Yaransa Biyu

JARABTA: Cikin Kwanaki Uku A Jere, Ya Rasa Matarsa Da Yaransa Biyu

Duk Labarai
JARABTA: Cikin Kwanaki Uku A Jere, Ya Rasa Matarsa Da Yaransa Biyu. Wannan bawan Allah mai suna Adamu Manzo ya gamu da jarabawar rashi. Shekaran jiya Lahadi babban d’ansa ya rasu aka yi masa jana’iza jiya Litinin, bayan an dawo daga makabarta jaririn da aka haifa masa da kwana d’aya ya rasu shi ma aka yi jana’izar sa, inda a jiya Litinin din, Allah mai yin yadda Ya so sai kuma ga shi an wayi gari da rasuwar matar sa wacce ita ce mahaifiyar yaran guda biyun da suka rasu. Tuni aka yi mata sallar jana’iza a safiyar yau Talata a unguwar Dawaki Kofar Sarkin Doya, dake jihar Gombe. Hakika wannan jarrabawa ta girmama matuka. Allah Ya gafarta musu.
Wata Sabuwa An gano cewa Hafsat Lawancy ba ta san namiji ba virgin ce

Wata Sabuwa An gano cewa Hafsat Lawancy ba ta san namiji ba virgin ce

Duk Labarai
Wata kungiya dake ikirarin ta matane masu tsafta wanda basu san Namiji ba wanda ake kira da Virgin a turance tace ta binciki Hafsat Baby ko Hafsat Lawancy wadda Bidiyonta tsirara ya bayyana. Kungiyar tace ta gano Hafsat bata san Namiji ba, Virgin ce. https://twitter.com/softsopheee/status/1838272662197395732?t=PONLSkozEMD_3yxROuZ3wA&s=19 Kungiyar ta kuma ce tuni ta baiwa Hafsat shahada dake nuna cewa ita virgin ce bata san Namiji ba.
Bidiyon tsiraicin hafsat baby: Ji Abinda Sheikh Aminu Daurawa yayi da Bidiyon

Bidiyon tsiraicin hafsat baby: Ji Abinda Sheikh Aminu Daurawa yayi da Bidiyon

Duk Labarai
A safiyar Litinin ce Sheikh Daurawa ya wallafa bidiyon Hafsat Baby tare da wasu mata da hukumar ta kama. Wasu majiyoyi a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano sun tabbatar wa Aminiya cewa Hafsan Baby tana tsare a hannun hukumar. Sai dai sun ƙi su bayyana lokacin da hukumar ta cika hannu da jarumar TikTok ɗin. Aminiya ta lura cewa bayan kimanin sa’o’i biyu, Sheikh Daurawa wanda a halin yanzu yake ƙasar Jamus, ya goge sakon bidyon kamen Hafsat. Ana iya tuna cewa a kwanakin baya hukumar ta sanar cewa an yi kutse a shafinta, lamarin da ya sa a halin yanzu ba za iya dogaro da wani daga shafin ba. Aminiya ta yi ƙoƙarin zantawa da jami’an Hisbah kan kamen Hafsat Baby, amma hakan bai samu ba. Jami’an da muka tuntuɓa sun bayyana cewa kasancewar Litinin ɗin ranar hutun Takutaha ce da Gwamna...
Ina baiwa gwamnati Shawarar ta cire tallafin man fetur gaba daya>>Dangote

Ina baiwa gwamnati Shawarar ta cire tallafin man fetur gaba daya>>Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa,yana baiwa gwamnatin tarayya shawarar cire tallafin man fetur gaba daya. Dangote ya koka da cewa farashin gas a Najeriya na da sauki matuka wanda na kasar Saudiyya ma yafi na Najeriya tsada. Yace kasashe ciki hadda saudiyyar duk sun cire tallafin man fetur din amma an bar Najeriya a baya. Dangote ya bayyana hakane a wata hira da kafar Bloomberg ta wallafa. Yace kuma cire tallafin man da baiwa matatarsa dama zai sa a san ainahin yawan man fetur din da 'yan Najeriya ke sha wanda a yanzu ba'a sani ba.
Hotuna: Ganin Jarumin Fim Din Hausa, Haruna Talle Maifata A Wajen Sana’ar Jari Bola Ta Jawo Cece-Kuce A Kafar Sadarwa

Hotuna: Ganin Jarumin Fim Din Hausa, Haruna Talle Maifata A Wajen Sana’ar Jari Bola Ta Jawo Cece-Kuce A Kafar Sadarwa

Duk Labarai
Ganin Jarumin Fim Din Hausa, Haruna Talle Maifata A Wajen Sana'ar Jari Bola Ta Jawo Cece-Kuce A Kafar Sadarwa. Wasu da suke cin karo da bidiyon sa a bakin sana'ar ta jari bola, har cewa suke kawai yana yi ne domin ya jawo cece-kuce ko kuma neman karin followers, amma ba gaskiya bane. Yayin da wasu kuma suke zargin cewa fim ne kawai yake yi, domin daukakar sa a fim ta fi karfin ya yi harkar jari bola.