Wednesday, May 13
Shadow

Duk Labarai

Abubuwa bakwai da Trump ya ce zai yi a matsayin shugaban Amurka

Abubuwa bakwai da Trump ya ce zai yi a matsayin shugaban Amurka

Duk Labarai
Donald Trump na kan hanyar komawa fadar White House bayan da ya alƙawarta kawo ƙarshen wasu matsaloli ciki har da batun 'yan cirani, da tattalin arziki, da yaƙin Ukraine. Da alama ya samu ɗimbin magoya baya sakamakon manufofinsa na siyasa, musamman a majalisar dokokin ƙasar bayan da jam'iyyarsa ta Republican ta sake ƙwace iko da majalisar dattawan ƙasar. A jawabin murnar lashe zaɓe da ya gabatar, Mista Trump ya sha alwashin ''yin mulkin bisa taken: 'Cika alƙawuran da muka ɗauka'. Amma a wasu fannonin, ya bayar da taƙaitaccen bayanin yadda zai cimma manufofin nasa. A lokacin da kafar yaɗa labarai ta Fox News ta tambaye shi a 2023, ko zai yi amfani da kujerarsa ta hanyar da ba ta dace ba, ko muzguna wa 'yan adawar siyasa? Sai ya ce ba zai yi ba, ''in ban da a ranar farko''. "A...
Yadda manoma ke kwana a gonaki domin gadin amfanin gonarsu a jihar Yobe

Yadda manoma ke kwana a gonaki domin gadin amfanin gonarsu a jihar Yobe

Duk Labarai
A Najeriya, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda tsananin sata ke tilasta manoma fara kwana a gonakinsu domin gadi saboda yadda ɓarayi suka addabe su da satar amfanin gonakinsu. A jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas - inda aka samu rahoton ƙamarin lamarin - manoma da dama sun fara tarewa a gonakinsu ne musamman a cikin dare, wasu kuma aka tilasta musu su girbe amfanin ko da kuwa ba su isa girba ba saboda gudun kada su yi asara baki ɗaya. Daga cikin ƙananan hukumomin da matsalar ta fi ƙamari akwai Gujiba, da Damaturu, da Gashuwa, da sauransu. Lamarin ya kai ga wasu manoman na ɗaukar hayar mutane domin taya su gadi a gonakinsu, inda suke kwana ido biyu. Wannan matsala ba za ta rasa nasaba da yanayin da ake ciki a Najeriya ba na tsadar rayuwa, da hauhawar farashin kayan masar...
Nan da shekarar 2027 zamu gyara wutar lantarki ta yanda za’a rika samunta tsawon awanni 20 kullun>>Gwamnatin Tarayya

Nan da shekarar 2027 zamu gyara wutar lantarki ta yanda za’a rika samunta tsawon awanni 20 kullun>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace nan da shekarar 2027 zata samar da wutar Lantarki ta awanni 20 kullun. Saidai tace sharadin hakan shine sai ta samu maau zuba jari a bangaren Fetur da iskar gas wanda a yanzu babu su sosai. Me baiwa shugaban kasa shawara akan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana haka a wata ziyara da ta kai kasar Africa ta kudu. Tace za'a mayar da hankali ne wajan samarwa Birane da masana'antu karfin wutar lantarkin.
Da Duminsa: Wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis

Da Duminsa: Wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis, 7/11/2024. Hutudole ya samu rahoton cewa wutar lantarkin ta lalace ne da misalin karfe 11:20am na yau Alhamis. Hukumar Nigeria National Grid ce ta tabbatar da hakan Wannan ne karo na biyu da wutar ta lalace a cikin satin da muke sannan karo na 12 a cikin wannan shekarar da muke ciki.
Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Duk Labarai
Mataimakin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin ya sanar da komawar Tauraruwar Fina-finan Hausa, Asma'u Abdullahi Wakili zuwa jam'iyyar APC. Ya wallafa hakane a shafinsa na zada zumunta inda ya yi mata maraba zuwa jam'iyyar APC. https://twitter.com/barauijibrin/status/1854270065547329955?t=7dvUTEwRZF-CKrPmAxoNAQ&s=19 Asma Wakili dai Hadimace ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf saidai ta ajiye mukamin nata inda ta kuma fice daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar APC. Sanata Barau yace Asma Wakili ta sanar da ficewarta daga NNPP a yayin ziyarar data kai masa a Abuja. Barau ya kara da cewa Asma Wakili ta bayyana ayyukan alkhairi na jam'iyyar APC ne ya jawo ta zuwa jam'iyyar. Yayi kira a gareta data zama jakadiya ta gari ga Masana'antarta ta Kannywood, Jam'iyy...
Mata basu son yin aiki da mata a matsayin oganninsu a Ofis shiyasa ake samun irin Mutuminnan na nasar Equatorial  Guinea masu yin lalata dasu>>Sanata Shehu Sani

Mata basu son yin aiki da mata a matsayin oganninsu a Ofis shiyasa ake samun irin Mutuminnan na nasar Equatorial Guinea masu yin lalata dasu>>Sanata Shehu Sani

Duk Labarai
Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana ra'ayinsa akan mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da mata da yawa ya kuma dauki Bidiyon faruwar lamarin. Sanata Sani yace Dalilin da yasa ake samun irin mutumin masu lalata da matan mutane a Ofis shine mata basu son mata 'yan uwansu su zama ogannin su. https://twitter.com/ShehuSani/status/1854454657164156931?t=Y3ueoL-V8O9o9aKXhIBBWw&s=19 Lamarin mutumin ya dauki hankula sosai inda akai ta Allah wadai dashi inda wasu suka rika yaba masa.