Rahotanni sunce wannan dalibar jami'ar UNIBEN dake jihar Edo an daketa aka yi mata fyade sannan aka kasheta.
Rahoton yace bayan da aka mata wannan danyen aiki, an kai gawarta kusa da gidansu aka ajiye cikin jini.
'Yan Uwanta na neman wanda suka mata wannan danyen aiki ruwa a jallo dan su fuskanci hukunci.
Gwamnan jihar Legas Babajide kenan a wadannan hotunan inda yake dafa abinci da kansa.
Ya yi hakanne ranar tunawa da Iyaye Maza a Duniya dan ya nuna bajintarsa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Mahmud Adam mai shekaru 43 da laifin satar mota, tare da gano motar kirar SUV da aka sace a karamar hukumar Gwaram.
DSP Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jigawa, ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar, 15 ga watan Yuni.
A cewar Shiisu, kama barawon ya biyo bayan rahoton sace wata mota kirar Honda CRV mai lamba DKD 10 AG mallakin Wani Abba Yahya daga garin Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano.
Ya ce motar tana kan hanyar zuwa Maiduguri jihar Borno.
Ya bayyana cewa, jami’in ‘yan sanda (DPO) na Gwaram tare da tawagarsa sun tare motar kirar SUV akan hanyar Sara zuwa Darazo.
SHiisu ya ce tuni aka mika wanda ake zargin da ...
Tauraron dan Tiktok, Mai Wushirya kenan a wannan bidiyon nasa da ya dauki hankula inda aka ganshi a Saudiyya wajan jifar Shedan.
https://www.tiktok.com/@realaedrees1/video/7381020482016906501?_t=8nGo8UQtRh7&_r=1
Ya rika tsalle yana yi wanda hakan ya dauki hankula.
Laila Usman wadda ta yi suna wajan taimakon marasa karfi da kuma Kasuwanci kenan a wadannan hoton inda suka sha kwalliyar Sallah da mijinta:
https://twitter.com/Laylahaliothman/status/1802378275341176911?t=S-ob2mxI4Gf3GBwCz1SFqQ&s=19
Dubban musulmai ne suka halarci Sallar Idi a Birnin Moscow na kasar Rasha.
https://twitter.com/GlobeEyeNews/status/1802314921830723649?t=_TPf-IvSllyhhKFtDwxsfg&s=19
Wani tsohon Bidiyo na Nazir Ahmad sarkin Waka ya dauki hankula a shafukan sada zumunta inda aka ganshi yana waka.
An dai alakanta Bidiyon da cacar bakin data faru tsakanin Naziru da 'yan Cryptocurrency.
https://twitter.com/Sarki_sultan/status/1801689450407153913?t=-OBcTlZ4iLyr0blpkOjhrw&s=19
Ko me zaku ce?
Wannan hoton ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta inda aka ga wani matashi yana daukar hoto yayin da ake Sallar Idi.
https://twitter.com/ibrahimtashboi/status/1802439160084759037?t=F6_AUnKPRIIrE9PpVca8Aw&s=19
https://twitter.com/EmesDos1/status/1802417436966174863?t=OPElzhGrtqNv7JhtzFBY9A&s=19
https://twitter.com/Abbakr_Abbaty/status/1802376022802702542?t=LVT3XMoZKbhlpN7KJPeI5Q&s=19
https://twitter.com/jiddah_mk/status/1802402291959373960?t=0fx1YU9ewy-FK_it8Mat9w&s=19
https://twitter.com/ummer_zeee/status/1802375684930589145?t=k1LWW10JPU0euYreEMjOqg&s=19
Hoton ya nuna maza da mata a yamutse a waje daya ana Sallah sannan wasu na cewa ma ba'a daidaita sahu ba.
Hoton ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.
Yanzu haka dai wani tsohon ministan lantarki kuma tsohon mataimakin gwamna a jihar Yobe, ya ce babban sirrin zama mataimakin gwamna da gwamnan kansa shi ne yin gaskiya da riƙon amana da kuma biyayya.
Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce duk da yake tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi muƙamin mataimakin gwamna, amma kuma bai tanadar masa wani taƙamaiman aiki ba, don haka “in dai kana so ka yi, ka zauna kawai. Abin da gwamna ya ce ka yi, ka yi. In ya ce kar ka yi, ka bari”.
A cewarsa: “Ba zancen kai Mataimakin gwamna (ne ba), ai tare muka je mu kai kamfen, ai tare muka je! Ai gwamnatin, tsarin mulki ne yake ajiye ta, to kai kuma tsarin mulki ba abin da ya ba ka”.
Tsohon Ministan ya Bayyana hakan ne a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya albarkacin cikar...