Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi tsalle ya sauka a kasa daga kan wani Dandamali.
An ga jami'an tsaron sa sun kamashi inda ya sauka a hankali.
https://twitter.com/i/status/2083272497131123169
A yaune dai Rahotanni suka watsu cewa, Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya saki matarsa Maimuna shekara daya bayan aurenta.
Hakan ya zowa mutane da mamaki musamman ganin cewa dama a baya ana zargin Adam A. Zango da auri saki.
Maimuna dai ta fito ta tabbatar da cewa, Adam A. Zango ya saketa inda tace kadararta kenan.
A yanzu kuma kafar AGG Media ta wallafa wata Hira da ta yi da Adam A. Zango amma bai yi magana akan maganar sakin auren nasa ba.
https://www.tiktok.com/@agg_multimedia_services/video/7668706556971715847?_r=1&_t=ZS-98UsYPULkqi
Rahotanni sun bayyana cewa, Adam A. Zango ya saki matarsa Maimuna shekara daya bayan auren.
Maimuna a hirar da aka yi da ita a gidan talabijin na Kosawa ta tabbatar da cewa aurenta ya mutu.
Tace Kaddararta kenan ita da Adam A. Zangon.
Saidai bata bayyana dalilin mutuwar auren nata ba.
https://www.tiktok.com/@kosawa_sadiya/video/7668706793350270229?_r=1&_t=ZS-98UoCvp3U2e
Bidiyon Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma Wakili kenan da ta yi shiga cikin kayan Kungiyar Barcelona da ya dauki hankali.
Wasu sun yaba da Bidiyon nata inda wasu suka kush3.
https://www.tiktok.com/@asmee_wakili/video/7668428805438000391?_r=1&_t=ZS-98UnEWzPm1F
Wannan Wani Bidiyo ne da ya nuna yanda aka raba abinci a wajan wani Biki da ya dauki hankula.
Da yawa dai sun ce an yi abin girma a wajan Bikin.
https://twitter.com/i/status/2083155756455457129
An ga Bidiyon wasu 'yan Arewa dake Rayuwa a Lagos a wani yanayi mara kyau.
An ga gidan nasu ruwa yayi ambaliya a cikinsa, sai sun dage rigunansu suke iya tafiya a ciki.
Da yawa sun bayyana rashin jin dadin hakan.
https://twitter.com/i/status/2082947359940436293
'Yan Shi'a sun fara Tattaki na cikar Kwanaki 40 da shahadar Hussain AS.
An ga na bangaren Kano da suka fito inda suka Nufi Zaria.
https://www.tiktok.com/@mahdy_na_zakzaky/video/7668275135228513554?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7668275135228513554&source=h5_m×tamp=1785496243&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7665740753532061457&share_link_id=29ff8330-b273-43bb-a1c5-e4de1e71c582&share_app_id=1233&ugbiz_name=MAIN&ug_btm=b6880%2Cb2001&sp_root_share_link_id=29ff8330-b273-43bb-a...
Farouk Abuja dake yawan sukar manyan mutane a shafinsa na sada zumunta ya shiga hannun jami'an tsaro.
A baya dai an rika cewa an kamashi wasu basu yadda ba inda daga nan ne sai ga Bidiyon sa ya bayyana a kafafen sada zumunta a hannun jami'an tsaro.
Aminu J Town wanda shima sun taba Bugawa da Farouk Abuja ya bayyana cewa, Lauyan Ministan Tsaro Christopher Musa ne yasa aka kama Farouk Abuja saboda ci masa mutunci
Sannan yace dalili kenan da yasa shima wani babban soja da ya dade yana ciwa mutunci ya fito yake neman hakkinsa akan Farouk Abuja.
J town yace da 'yansanda suka kama Farouk Abuja ya musu ihun wai sun saceshi ne bai san inda zasu kaishiba.
Saida suka tsaya sukawa mutane bayanin gaskiya akan Lamarin.
Wannan wasu matan Kiristoci ne da aka ga suna Fareti wanda ya dauki hankula a kafafen sada zumunta.
Da yawa Bidiyon ya basu Dariya.
https://twitter.com/i/status/2082903469761900861