Wasu mata da suka yi fada akan namiji a wani shagon sayar da magani sun dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta.
https://twitter.com/Postsubman/status/1838454869155283302?t=f4LSRFRBI-dJivlBLSKVgQ&s=19
Dayar matar ta cirewa 'yar uwarta yatsa wanda hakan ya jawo cece-kuce.
Wannan hoton ya nun yanda aka daure wani bawan Allah a bayan mota da igiya a Kano.
https://twitter.com/Abdulilu1/status/1838232683744293205?t=tCb9Iq7b0wAsGNRIJ3Fv7Q&s=19
Wasu dai sun daukeshi abin dariya inda wasu ke cewa ba abin dariya bane cin zarafine.
Ganin Jarumin Fim Din Hausa, Haruna Talle Maifata A Wajen Sana'ar Jari Bola Ta Jawo Cece-Kuce A Kafar Sadarwa.
Wasu da suke cin karo da bidiyon sa a bakin sana'ar ta jari bola, har cewa suke kawai yana yi ne domin ya jawo cece-kuce ko kuma neman karin followers, amma ba gaskiya bane. Yayin da wasu kuma suke zargin cewa fim ne kawai yake yi, domin daukakar sa a fim ta fi karfin ya yi harkar jari bola.
An Ba Su Madarar Yougot A Matsayin Gwarazan 'Yan Wasa A Wasannin Gasar Kwallon Ta Birnin Kudu Dake Jihar Jigawa.
Wani kamfani ne ke daukar nauyin bada kyautar domin karfafawa matasan 'yan wasan.
Me za ku ce?
Daga Imam Murtadha Gusau
Wasu jajirtaccin matasa 'yan sakai wadanda suka sadaukar da rayuwar su tare da lokacin su, wurin kariyar al'ummah, sune suka farmaki Kacallah Black tare da tawagar yaran shi, a daidai lokacin da suka samu labarin cewa shararren dan ta'adda Black ya fito zai je wurin wata aika-aika, an samu nasarar kashe Black da yaran shi akalla kusan su 10, a wani yanki na dajin mai tashi dake yamma ga 'Yar Tashar Sahabi dake kan hanyar Dansadau, an samu nasarar kwato mashuna da bindigogi tare da alburusai na wannan dan ta'addar da na yaran shi.
Rahotannin da suke zo muna daga mazauna yankin 'Yar Tashar Sahabi, suna nuni da cewa wannan gagarumar nasara ce aka samu domin wannan dan ta'addar shine ya addabi yankin hanyar Dansadau zuwa Magami da kuma wasu bangarora na yankunan....
Hezbollah ta harba gomman rokoki zuwa kudancin Isra'ila, a cewar ƙungiyar a wata sanarwa.
Ta ce ta far wa shingayen sojoji da kuma wuraren ajiye makamai ta hanyar amfani da makamai masu linzami,a wani matsayin martani ga hare-haren da Isra'ilar ta kai kudancin ƙasar.
A wata sanarwa ta daban, dakarun tsaron Isra'ila (IDF), sun ce an harba rokoki aƙalla 35 daga Lebanon kuma hakan ya shafi shingayensu.
An jikkata wani mutum mai shekara 50 a yankin Galilee, a cewar sojoji Isra'ila.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojin saman ƙasar sun kakkaɓo rokoki da dama da Hezbollah ɗin ta harba yayin da wasu kuma suka yi lahani a wasu yankuna kusa da garin Ami'ad.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin jihar ta karɓi kusan naira biliyan huɗu da rabi daga cikin fiye da naira biliyan 13 da aka yi musu alƙawari a matsayin tallafi ga waɗanda ibtila'in ambaliya ya shafa a Maiduguri.
"...naira 4,441,494,902.81 ne suka shigo hannunmu daga cikin alƙawuran N13,195,500,000 da aka yi mana. Za mu ci gaba da sanar da jama'a duk lokacin da aka samu ƙarin shigowar kuɗi" In ji gwamna Zulum.
Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kafa kwamitin mutum 35 da zai kula da raba wannan tallafi ga waɗanda al'amarin ya shafa.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani ya fitar, ya wallafa a shafin X na gwamna Zulum, gwamnan ya ce kwamitin zai ƙunshi wakilai daga hukumomi da ...
Wani tsoho dakw rawa a wajan Maulidi ya dauki hankula sosai bayan da aka ga bidiyonsa a shafukan sada zumunta.
Kalli Bidiyon a kasa:
https://twitter.com/bb_khamees/status/1837826273663414293?t=R_hZyH8aRHUgtZ0lNpgtmQ&s=19
Wasu dai na ganin hakan bai dace ba inda wasu ke cewa duk cikin shauki ne.
Ma'aikacin Asibiti a Zaria ta jihar Kaduna, Musa A Bello da ya ajiye aikinsa saboda tsammanin Hamster Kombat zasu bashi kudi da yawa yayi Allah ya isa.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace wanda ya bashi shawarar yin Hamster Kombat yace masa da haka Bitcoin ya fara.
Yace abin takaici ne abinda hamsters Kombat suka bashi wanda bai taka kara ya karyaba inda ya ajiye aikinsa na shekara da shekaru saboda tsammanin zaau bashi kudi masu yawa.
Ya kara da cewa yanzu ta ina zai fara, daga barazanar da ake masa a wajan aiki ko da dariyar da jama'a ke masa?
Yace rayuwarsa a yanzu ta shiga halin rashin tabbas amma yace in Allah ya yarda zai sake samun wani aikin.
https://twitter.com/pharm_musa/status/1837710459480199366?t=kxuLRfll1IXCLsPQWbEaug&s=19
Yace ba za...