Wednesday, July 1
Shadow

Duk Labarai

Man Fetur din matatar man Dangote ba zai ishi Najeriya ba dan haka zamu ci gaba da Shigo da man fetur daga kasar waje>>inji NNPCL da ‘yan kasuwar Man Fetur

Man Fetur din matatar man Dangote ba zai ishi Najeriya ba dan haka zamu ci gaba da Shigo da man fetur daga kasar waje>>inji NNPCL da ‘yan kasuwar Man Fetur

Duk Labarai
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa,Man fetur din da matatar man Dangote ke samarwa ba zai ishi Najeriya ba dan haka zata koma ta ci gaba da shigo da Man fetur daga kasashen waje dan cike gibin suran man fetur din da Dangote bai iya samarwa. Kamfanin na NNPCL yace matatar man fetur ta Dangote ta basu Lita Miliyan 10.3 ta man fetur din Me magana da yawun NNPCL, Olufemi Sonoye ya bayyana cewa, suna fuskantar karancin lita miliyan 65. Yace tun a farko an yi tsammanin rika samun lita miliyan 25 ne a kullun daga matatar man ta Dangote amma hakan bai samu ba. Itama dai kungiyar 'yan Kasuwa masu zaman kansu, IPMAN ta hannun shugabanta, Abubakar Garima ta bayyana cewa, man na Dangote ba zai ishi Najeriya ba sai an ci gaba da shigo da man daga kasagen waje.
Dubu saba’in din da aka kara mana a matsayin mafi karancin Albashi a yanzu bata da amfani Saboda farashin Man fetur>>NLC

Dubu saba’in din da aka kara mana a matsayin mafi karancin Albashi a yanzu bata da amfani Saboda farashin Man fetur>>NLC

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa karin albashin da aka mata na Naira Dubu 70 bashi da Amfani a yanzu saboda tashin farashin man fetur. Kungiyar ta bayyana hakane ta bakin shugaban ta, Joe Ajaero inda yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yaudaresu suka amince da naira 700 a matsayin mafi karancin Albashi. A yanzu dai,Kungiyar ta Kwadago zata gana da shugaban kasa dan neman mafita kan lamarin.
TIRKASHI: Wani likita dake Zaria ya ajiye aikin shi saboda Miniɲg din HAMSTER

TIRKASHI: Wani likita dake Zaria ya ajiye aikin shi saboda Miniɲg din HAMSTER

Duk Labarai
TIRKASHI: Wani likita dake Zaria ya ajiye aikin shi saboda Miniɲg din HAMSTER. Ma'aikacin Asibiti mai suna Pharm Musa A Bello Zaria, ya bayyana takkaddar ajiye aikin shi a safinshi na Facébooķ inda ya bayyana cewa ya ajiye aikin nashi ne kan saran tsammanin fashéwar HAMSTER wanda zai zama miloniya ya bude kamfanoni da kudin Mining din tare da daukar ma'aikata aiki a karkashin kamfanin nashi. Wace shawara zaku bashi?
Kalli Hotuna: Jami’in Tsaron Gidan yari ya kashe abokin aikinsa saboda abinci a jihar Bauchi

Kalli Hotuna: Jami’in Tsaron Gidan yari ya kashe abokin aikinsa saboda abinci a jihar Bauchi

Duk Labarai
Marigayi Aliyu Abubakar Ciroma. Jami'in tsaron gidan yari a garin Burra dake karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi ya kashe abokin aikinsa sabosa Abinci. Lamarin ya farune tsakanin Aliyu Abubakar Chiroma da Abokin aikinsa, Kabiru Abubakar wadanda suka jami'an tsrone na gidan yari koma kowa ya sansu Abokan junane. Ranar da abin zai faru sun je cin abinci tare sai Chiroma ya ciro abincin nasa inda Kabiru yace zai ci, anan rigima ta kaure tsakaninsu inda Chiroma yace ba zai ci mai abinci ba. A hakane sai Kabiru yawa Ciroma karo da kai, inda nan take ya fadi baya motsi. An garzaya dashi babban Asibitin Burra inda likitoci suka tabbatar ya mutu. Tuni aka kama Kabiru. Shugaban karamar hukumar Ningi, Hon Nasiru Zakari ya tabbatar da faruwar lamarin inda shima kakakin hukumar gid...
Ji abinda Bello Turji yayi bayan da yaga sojoji sun kashe me gidansa

Ji abinda Bello Turji yayi bayan da yaga sojoji sun kashe me gidansa

Duk Labarai
Tun bayan da sojojin Najeriya suka kashe Buzue gidan Bello Turji, Turjin ya aka rasa inda ya shige. Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka, Bello Turji da mayakansa sun canja maboya. A baya suna zaunene a wani guri dake kusa da Tsafe. Amma yanzu sun tashi daga nan inda suka koma Munhaye duk a cikin jihar ta Zamfara. Babban me kawo rahotanni akan harkar tsaro, Zagazola makamane ya bayyana hakan.
Bidiyo: Kalli Yanda Sojan Ruwa wanda matarsa taje Berekete Family akan an daureshi yaki bayar da Bindigar sa

Bidiyo: Kalli Yanda Sojan Ruwa wanda matarsa taje Berekete Family akan an daureshi yaki bayar da Bindigar sa

Duk Labarai
Bidiyon sojan ruwa, Seaman Haruna wanda matarsa taje Brekete Family tana korafin an daureshi tsawon shekaru 6 ya bayyana inda aka ga yanda yaki bayar da Bindigarsa. Haruna Sojan ruwane amma sojojin kasa ne suka zo zasu kwace masa bindiga. Dalilin da yasa kenan yaki amincewa. https://twitter.com/ZagazOlaMakama/status/1836705544880390546?t=4bL54sBRrLWaVWsvPzIWag&s=19 A bidiyon an ga yanda yake kokawa da sojojin yayin da suke kokarin kwace masa Bindigar amma yaki. Daga karshe dai an kwace Bindigar aka kaishi aka daure.
Matawalle na da hannu a aikin ƴan fashin jeji, in ji Gwamnan Zamfara

Matawalle na da hannu a aikin ƴan fashin jeji, in ji Gwamnan Zamfara

Siyasa
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi zargin cewa magabacinsa, Bello Matawalle, na da hannu dumu-dumu a aiyukan ƴan fashin jeji da suka addabi jihar. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa da ya ke magana a wani shirin siyasa na gidan talabijin na TVC a daren jiya Laraba, gwamnan ya yi ikirarin cewa, bisa bayanan da su ka samu, magabacinsa ya jagoranci gwamnatin da ke hada kai da ƴan fashin jeji su na aikata ta'addanci. Lawal ya kuma zargi gwamnatin da ta shude a karkashin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne karamin ministan tsaro da karkatar da kudaden jihar da kuma yin sakaci da harkar tsaro a jihar. “Eh, akwai batutuwa da yawa a baya daga gwamnatin da ta gabata. A gaskiya, bari in fadi wannan sarai: da nine shi (Matawalle) zan yi murabus in fuskanci duk wani zargi da ake min, haka...
Sheikh Nura Khalid Ya Halarci Taron Mabiya Shi’a Mai Taken ‘Makon Hadin Kai’

Sheikh Nura Khalid Ya Halarci Taron Mabiya Shi’a Mai Taken ‘Makon Hadin Kai’

Duk Labarai
Taro ne dai wanda shugaban mabiya Shi'a na Nijeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ke jagoranta, an gudanar da shine a jiya Laraba a Abuja, inda ake gudnarwa domin haɗa kan malamai daga ɓangarori daban-daban dake fadin kasa baki daya, kama daga musilmai da Kìrìstòcì, inda kowane banhare ke amsa gayyata tare da yin jawabai da suke da alaƙa da haɗin kai da zaman lafiya. An gabatar da taron ne a Abuja inda malamin ya yi Magana akan Soyayyar Manzon Alĺàh SAW tare da amfanin hadin kai. Me za ku ce? Daga Abba Abdulaziz Fari Funtua
Matar Shugaba Tinubu Ta Bada Gudummuwar Naira Milyan 500 Ga Al’ummar Maiduguri

Matar Shugaba Tinubu Ta Bada Gudummuwar Naira Milyan 500 Ga Al’ummar Maiduguri

labaran tinubu ayau, Siyasa
Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 500 ga gwamnatin jihar Borno ta hanyar shirinta na Renewed Hope Initiative domin tallafawa wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Maiduguri. Uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima ta wakilci uwargidan mataimakin shugaban kasa kuma mataimakiyar shugaban kungiyar Renewed Hope Initiative, Uwargidan shugaban kasar ta jajantawa al'ummar Borno bisa bala'in da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyi da rayuwa ¹. A yayin bayar da gudummawar a gidan gwamnati, Hajiya Nana Shettima ta yaba wa Gwamna Farfesa Babagana Umara Zullum bisa gaggauwa da gaggawar da ya dauka kan bala’in da kuma tallafin da aka ba wa wadanda abin ya shafa. Gwamnan ya nuna godiya ga Sanata Oluremi Tinubu bi...
Kwankwaso Ya Bada Gudunmawar Naira Milyan Hamsin Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Borno

Kwankwaso Ya Bada Gudunmawar Naira Milyan Hamsin Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Borno

Rabiu Musa Kwankwaso
Daga Abubakar Shehu Dokoki Ɗan Takarar Shugaban ƙasa, ƙarkashin Tutar Jam'iyyar NNPP a zaɓen daya gabata na 2023 Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bada wannan tallafin ne a wata ziyara ta musamman da ya kai jihar Borno domin jajanta musu bisa ambaliyar ruwan da ta yi sanadiyyar raba ɗaruruwan mutane da gidajensu. Kwankwaso ya miƙa wannan tallafi ne ta hannun Gwamnatin Jihar Borno.