Sunday, June 28
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa: Majalisar Tarayyar Najeriya ta nemi a canja tsarin mulki da zai baiwa shugaban kasa damar yin zango daya na shekaru 6

Da Duminsa: Majalisar Tarayyar Najeriya ta nemi a canja tsarin mulki da zai baiwa shugaban kasa damar yin zango daya na shekaru 6

Siyasa
Wasu 'yan majalisar wakilai sun nemi cewa, a canja tsarin mulkin Najeriya da zai baiwa shugaban kasa damar yin mulki na shekaru 6 wa'di daya. Sannan sun nemi a rika yin karba-karbar mulki tsakanin yankuna 6 da ake dasu a kasarnan. Dan majalisar daga jihar Imo, Ikenga Ugochinyere ne ya bayyana hakan inda yace idan shugaban kasa, Gwamnoni suka rika yin wa'adi daya na shekaru 6 kawao, za'a samu saukin kashe kudi da kuma yin aiki me kyau.
PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu

PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu

Siyasa
PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu Jam’iyyar PDP ta bayyana ranar Alhamis 26 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa karo na biyu a shekarar 2024. Idan za a iya tunawa, a taron farko da hukumar NEC ta gudanar a ranar 18 ga watan Afrilu,an tattauna batutuwan da suka hada da makomar mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Illiya Damagum, an daga shi zuwa taron NEC na gaba wanda aka shirya tun watan Agusta. Kungiyar ‘yan jam’iyyar ta Arewa ta tsakiya ta ce za a zabi dan takara daga shiyyar don kammala wa’adin tsohon shugaban Jam'iyyar na kasa, Dr. Iyiorchia Ayu, wanda ya yi murabus kusan shekaru biyu cikin wa'adinsa na shekaru hudu. Gabanin taron NEC na watan Satumba, jam’iyyar ta tsayar da ranar 27 ga wata...
ƳANZU-YANZU: Za a fassara huɗubar Arfa da Hausa, Cewar Sheikh Sudais

ƳANZU-YANZU: Za a fassara huɗubar Arfa da Hausa, Cewar Sheikh Sudais

Siyasa
Babban Limamin Masallatan Harami Sheikh Abdurrahman Sudais ya sanar cewa za a fassara hudubar Ranar Arafa kai-tsaye a cikin harshen Hausa da wasu harsuna 19 domin karuwar alhazai da sauran al'ummar Musulmi a fadin duniya. Sheikh Sudais ya ce ana sa ran sama mutum miliyan 100 za su saurari hudubar wadda Sheikh Maher Al Mu'ayqaly zai gabatar a Masallacin Namirah ta kafofin watsa labarai daban-daban.
Da Duminsa: Kungiyar Kwadago, NLC ta yi watsi da tayin Naira dubu suttin da biyu(62,000) ta bayyana ranar da zata ci gaba da yajin aiki

Da Duminsa: Kungiyar Kwadago, NLC ta yi watsi da tayin Naira dubu suttin da biyu(62,000) ta bayyana ranar da zata ci gaba da yajin aiki

Siyasa
Kungiyar Kwadago, NLC ta bayyana cewa bata akince da tayin Naira dubu 62 a matsayin mafi karancin Albashi ba. Tace kai ko dubu 100 ba zata amince dashi a matsayin mafi karancin Albashin ba, Kungiyar tace wannan kudi sun yi kadan wa ma'aikata su rayu ciki rufin asiri. Mataimakin babban sakataren kungiyar, Chris Onyeka ne ya bayyana haka a Channels TV yayin ganawa dashi ranar Litinin. Ya kuma ce kwaki 7 ko sati daya da suka baiwa gwamnati kan ta bayyana matsayinta ya kare ranar Talata, kuma idan gwamnatin ta dage akan hakan, zasu sake zama ranar talatar dan tsayar da matsaya kan ci gaba da yajin aikin. “Our position is very clear. We have never considered accepting N62,000 or any other wage that we know is below what we know is able to take Nigerian workers home. We will not nego...
An sace dalibai da wasu 25 a hanyar zuwa Nasarawa

An sace dalibai da wasu 25 a hanyar zuwa Nasarawa

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da mutane 25 da kuma wasu dalibai akan hanyar Abuja zuwa Nasarawa. Lamarin ya farune ranar Juma'a kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito kuma yawan wadanda aka yi garkuwa dasu sun kai 30. Direban motar dai ya kubuta inda ya kaiwa 'yansanda rahoton faruwar lamarin. Hukumar 'yansanda ta jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta,Rahman Nansel inda tace an kubutar da mutane 3 daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu kuma ana kan kokarin kubutar da sauran.
Kasar Rasha na takurawa ‘yan Afrika dake kasarta, ko dai su shiga aikin soja, su je yaki da Ukraine ko kuma ta dawo dasu gida

Kasar Rasha na takurawa ‘yan Afrika dake kasarta, ko dai su shiga aikin soja, su je yaki da Ukraine ko kuma ta dawo dasu gida

Siyasa
Rahotanni daga kasar Rasha na cewa, kasar na takurawa 'yan Afrika dake kasar shiga aikin soji dan yin yaki da kasar Ukraine. Rahoton jaridar Bloomberg ya bayyana cewa, kasar ta Rasha tana kuma takurawa hadda dalibai dake karatu a kasar. Saidai duk da haka wasu na baiwa jami'an tsaro cin hanci dan su kyalesu su zauna a kasar ba tare da su shiga aikin sojan ba ko kuma an dawo dasu gida ba. Yakin Rasha da Ukraine dai kullun sai kara kazancewa yake inda Ukraine din ke ci gaba da samun goyon bayan kasashen Yamma da Amurka.
Bai kamata Tinubu ya soki Gwamnatin Buhari ba saboda cewa yayi zai dora daga inda Buhari ya tsaya>>Buba Galadima

Bai kamata Tinubu ya soki Gwamnatin Buhari ba saboda cewa yayi zai dora daga inda Buhari ya tsaya>>Buba Galadima

Siyasa
Jigo a jam'iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, bai kamata shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dorawa Buhari ko wane irin laifi ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Sunnewsonline. Yace dalilin da yasa yace haka shine Tinubu yayi Alkawrin dorawa akan inda shugaba Buhari ya gama mulkinsa. Da aka tambayeshi ko me zai ce kan matsin rayuwar da ake ciki, Buba Galadima ya kada baki yace ai 'yan Najeriya ne suka siyowa kansu da kudinsu. Yace sai da ya gargadi mutane amma suka kiya.
Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Abuja, Tsaro
'Yansanda a Abuja sun bankado wata maboyar 'yan Bindiga dake gidan Dogo a cikin daji Kweti dake kusa da babban birnin tarayya, Abuja. Kakakin 'yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan ga manema labarai inda tace an bankado maboyar ne bayan samun bayanan sirri. An kama mutane 4 da ake zargi bayan da aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron. Dukansu sun amsa cewa su masu garkuwa da mutanene. An kubutar da wasu da suka yi garkuwa dasu inda aka mika su hannun 'yan uwansu.