Sunday, January 12
Shadow

Duk Labarai

Zanga-zangar karancin man fetur ta barke a Abuja

Zanga-zangar karancin man fetur ta barke a Abuja

Duk Labarai
Ranar litinin, 'yan Najeriya sun fara zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan karancin man fetur a Abuja. Kungiyar Coalition of Concerned Civil Society Organizations of Nigeria ce ta shirya zanga-zangar dan jawo hankalin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan ya magance matsalar karancin man fetur data kunno kai. Shugaban kungiyar, Comrade Aminu Abbas y dora alhakin karancin man fetur din akan shugaban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari.
Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane ta Tarayya, ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano

Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane ta Tarayya, ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano

Duk Labarai
Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane ta Tarayya, ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano. Aikin ginin gidajen da aka yi wa laƙabi da “Renewed Hope Estate” na wakana ne a ƙauyen Lambu da ke ƙaramar hukumar Tofa. Aikin ya haɗa da gina gida mai ɗaki biyu, ɗaki ɗaya, da kuma waɗanda ke da ɗaki uku. A lokacin da ya kai ziyara wajen aikin, Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aikin ke tafiya. Ya ce aikin ba ya sauri kamar yadda aka tsara tun da fari. Ya gargaɗi wanda aka bai wa kwantiragin da ya hanzarta ko kuma gwamnat ta ƙwace aikin daga hannusa. Ya kuma ce gwamnatin na son ganin an kammala aikin nan da ƙarshen shekara.” Kwantiragin, wanda manajan aikin Haruna Lawal ya wakilta, ya bai wa ministan tabbacin cewa za su ƙara ƙ...
YANZU-YANZU: Rundunar yan sandan Najeriya na neman wani bátưré ruwa a jallo bayan ta bakaɗo yana kitsa yadda za a yiwa Tinubu júyíɲ mulkí

YANZU-YANZU: Rundunar yan sandan Najeriya na neman wani bátưré ruwa a jallo bayan ta bakaɗo yana kitsa yadda za a yiwa Tinubu júyíɲ mulkí

Duk Labarai
Rundunar yan sandan Najeriya a yau Litinin ta saka cigiya tana neman wani bature dan kasar Birtáɲiya dake zaune a Najeriya Andrew Wynne (wanda aka fi sani da Andrew Povich ko Drew Povey), bisa zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu Rundunar ta ce tana da ƙwararan hujjjoji bisa zargin da take yi wa mutumin wanda ya kama haya a ginin hedikwatar kungiyar ƙwadago dake Abuja inda yake sayar da litattafai don yin badda kama, a haka yake ta kitsa mugun nufin nasa, sannan ya bude wasu wajajen kasuwanci Me zaku ce?
YANZU-YANZU: Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi Sun Fara Tattaunawa Domin Hadewa Waje Daya Don Tunkarar Zaben 2027

YANZU-YANZU: Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi Sun Fara Tattaunawa Domin Hadewa Waje Daya Don Tunkarar Zaben 2027

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Manya-manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, kwankwaso da Peter Obi na tattaunawa kan yiwuwar hadaka gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027. Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin. Abdullahi ya ce, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don ceto Nijeriya a cikin kangin da jam’iyyar APC ta cefa kasar a shekarar 2027. Ana dai ganin dunkulewar waje daya na da alaƙa da zaɓen shugaban kasa 2027 don kawar da gwamnatin APC kamar yadda masu sharhi suka bayyana. Me za ku ce kan wannan yunkuri?
HOTUNA: Kalli yanda magidanci ya kwakule idanun matarsa dan yin sihirin neman kudi

HOTUNA: Kalli yanda magidanci ya kwakule idanun matarsa dan yin sihirin neman kudi

Duk Labarai
Wani magidanci a jihar Abia ya danne matarsa ya kwakule mata idanuwa bisa niyyar yin kudin sihiri. Mutumin me suna Lawrence Uzor yana sana'ar Alminiyum ne. Lamarin ya farune a Adiele Estate dake karamar hukumar Umueze Ibeku in Umuahia ranar Asabar 24 ga watan Augusta. Mutumin dai yayi amfani da wuka ne ya kwakule idanun matar tasa yayin da take bacci. Me gidansu data ji ihu cikin dare ta yi kokarin kai dauki itama ya illatata amma daga baya an kamashi, inda su kuma wanda suka jikkata an garzaya dasu zuwa Asibiti. Uwar gidan gwamnan jihar, Mrs Priscilla Otti ta bayar da tabbacin daukar matakin da ya dace akan lamarin inda ta bayar da kudi dan a kula da wadanda suka jikkata.