Tsohon Shugaban kasa Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara daya akan mulki inda yace ‘yan Najeriya su bashi goyon baya
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya shugaban masa me ci murnar cika shekara guda akan mulki.
Ya bayyana hakane a wani sako da ya fitar.
Ya jawo hankalin mutane da su baiwa Tinubu goyon baya akan mulkin da yake yi.
Ya kuma yiwa Tinubun fatan kammala mulkinsa cikin nasara.







