Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dawo da taken Najeriya na daya daga cikin muhimman abubuwan da yake son yi a mulkinsa.
Ya bayyana hakane a yayin ganawa da kungiyar dattawan Najeriya, ACF.
Tinubun dai ya sakawa dokar data dawo da tsohon taken Najeriya hannu wanda hakan ya jawo cece-kuce inda mutane ke cewa ba wannan ne matsalar kasar ba.
Shugaba Tinubu ya kuma jawo hankali kan samun hadin kai a Najeriya.
Hukumar 'yansandan jihar Legas ta bakin tsohuwar kakakin hukumar, Dolapo Badmus ta bayyana cewa rashin iya taken Najeriya, kwakaki 3 bayan shugaban kasa ya saka shi a matsayin doka babban laifi ne.
Ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda take bayar da misalin wani me makaranta data sa a kama saboda yana rera tsohon taken Najeriyar.
Tace rashin iya taken Najeriyar cin amanar kasa ne.
Ta baiwa mutane shawarar su samu lauyoyi su musu karin bayani.
‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria signed and assented the New National Anthem into law and you are not able to recite it in a whole, then you are a suspect
I just passed through a private school and I could here them singing the old National Anthem! "Arise oh compatriots"! (We are...
Tsohuwar kakakin 'yansandan jihar Legas, Dolapo Badmus ta yi kiran a kama shugaban wata makaranta me zaman kanta da babban malamin makarantaar saboda rera tsohon taken Najeriya.
Ta bayyana cewa, ta zo wucewa ta kusa da makarantar ne sai ta ji suna rera tsohon taken Najeriyar.
Tace tuni ta yiwa 'yansanda magana kan a kamasu tare da gurfanar dasu a gaban kotu dan musu hukunci.
Tace kwanaki 3 bayan da shugaban kasa ya sakawa dokar canja taken Najeriyar hannu, duk wanda aka samu bai iyashi ba, to me laifi ne.
Tace kada wanda ya tambayeta laifin me suka yi, duk wanda ke da tambaya, ya samu lauya ya masa karin bayani.
Tace duk wanda bai iya sabon taken Najeriya ba, to yana cin amanar kasane.
‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria sign...
Britain's Prime Minister and Conservative Party leader Rishi Sunak reacts after bowling a ball during a Conservative general election campaign event at the Market Bosworth Bowls Club in Market Bosworth, central England, on May 28, 2024. (Photo by Alastair Grant / POOL / AFP)
Firai kinistan Ingila, Rishi Sunak ya bayyana cewa, ba lallai sai mutum na da karatun boko bane zai yi nasara a rayuwa.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta.
Screenshot
Saidai lamarin ya jawo cece-kuce sosai inda wasu suka goyi bayansa, wasu kuma suka ce hakan ba daidai bane.
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan dari biyar, $500 million dan karfafawa kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasa.
Hukumar BPE tace an ciwo bashinne dan magance matsalolin da suka mamaye kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasarnan.
Wakiliyar hukumar BPE, Amina Othman ce ta bayyana haka inda tace za'a yi amfani da kudadenne wajan sayo mitocin wuta da sauransu.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana damuwa kan halin 'yan siyasa na mantawa da mutane idan suka ci zabe.
Ya bayyana hakane ranar Alhamis a yayin ganawa da dattawan Arewa na kungiyar ACF bayan ziyarar da suka kai masa fadarsa.
Yace da mun ci zabe sai mu koma Abuja amma idan muna neman kuri'a mukan je gurin mutane.
Tinubu ya bayyana muhimmancin ganin cewa, gwamnatocin kananan hukumomi na aiki yanda ya kamata.
“People reside in the local communities. That is where they work, farm, and live. If the local governments are not effective in delivering services; as leaders, we must not hang on to the numbers.“Maybe we should look at recalibrating. What was good four years ago may not be good today. When we want the votes, we go to the locals; when we get the votes, we move to an...
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya zamo shugaban Amurka na farko da za a yankewa hukunci a kan tuhuma ta mugun laifi, bayan da masu taimaka wa alkali yanke hukunci suka same shi da laifi a tuhume-tuhume 34 da ake yi masa.
Dukkan tuhume-tuhumen na da alaka da karyar da ya yi a harkokin kasuwancinsa domin boye kudin da ya bayar na toshiyar baki a kan alakarsu da mai fitowa a fina-finan batsa wato Stormy Daniels a lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasar a 2016.
Da yake Magana a wajen kotun da ke Manhattan bayan samunsa da laifi, Donald Trump, wanda za a yankewa hukunci a watan Yuli mai zuwa, ya kira sakamakon zaman da aka yi a matsayin an yi masa almundahana da coge kuma hakan wani babban aibune.
Sannan ya kara da cewa al’umma za su yanke hukunci na gaskiya a ranar za...
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata.
Tinubu ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kungiyar dattawan Arewa ta ACF da yammacin ranar Alhamis.
Yace zai ci gaba da yin aiki iya kokarinsa dan ci gaban Najeriya.
Ya bayyana cewa, yana godewa 'yan majalisar zartaswarsa kan kokarin da suke amma zai rika dubawa yana tankade da rairaya dan gano wanda basa aiki yanda ya kamata dan canjasu.