Tinubu bai faɗi nawa albashi mafi ƙanƙanta zai kasance ba a jawabinsa
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta aike da ƙudiri ga Majalisar Dokokin ƙasar wanda zai kunshi adadin abin da aka amince da shi ya zama albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikata a "matsayin wani ɓangare na "dokokinmu" a shekaru biyar ko ƙasa da haka masu zuwa.
Shugaban wanda ya faɗi hakan ne a yayin jawabinsa ga ƴan Najeriya albarkacin ranar dimukraɗiyya, ya ce lallai yana sane da halin matsin tattalin arzikin da 'yan najeriyar ke ciki. To sai dai ya nemi "yan ƙasar da su tallafa wajen cimma "dimukraɗiyyar da za ta tabbatar da cigaban tattalin arziki."
Ƴan Najeriya dai sun yi fatan jin ƙarin albashin da suka samu daga bakin shugaban nasu a jawabin nasa na safiyar Talata.
A ranar Litinin ne dai kwamitin mutum 37 da aka kafa kan albashin mafi ƙanƙanta ya miƙa rahotonsa bayan kwashe kima...