Wednesday, January 15
Shadow

Tsaro

Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba’a gano inda take ba

Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba’a gano inda take ba

Katsina, Rarara, Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, awanni 24 bayan yin garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, Rarara har yanzu, ba'a gano inda take ba. Kakakin 'yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa an kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da mahaifiyar Rarara din amma har yanzu ba'a gano inda take ba. Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan Bindigar da suka je yin garkuwa da mahaifiyar Rarara sun je ne a kafa tike da muggan makamai suka shiga gidanta suka kamata. Rahoton yace Bata musu gaddama ba kuma babu wanda ya tunkaresu saboda muggan makaman da suke dauke dasu. Daily Trust tace ta nemi jin ta bakin Rarara amma bata yi nasara ba saboda wayoyinsa duk a kulle kuma an aika masa da sakon waya amma bar bayar da amsa ba.

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 8 a Maiduguri da jikkata wasu da dama

Borno, Tsaro
Rahotanni daga jihar Borno na cewa harin Bom ya kashe akalla mutane 8 da jikkata mutane da dama. Harin wanda na kunar bakin wakene mahara 4 ne suka kaishi kuma rahoto yace dukansu sun mutu. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da mutane 8 ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya bayyana cewa lamarin ya farune da misalin karfe 3:40 na safiyar yau,Rabar, 29 ga watan Yuni. Rahoton yace wata mata dake goye da yaro ta tayar da bom din a tashar motar Mararraba dake T. Junction dake garin Gwoza. Matar da dan da take goye dashi da wasu 6 sun mutu. A bangaren jaridar Premium times kuwa, tace mata 4 ne suka tayar da bamabamai a bangarori daban-daban na jihar wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba'a kai ga tantance yawansu ba c...

Ƴań Bìñďîģà Sun Sácé Mąhaifiýar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara A Gârin Kahutu Dáke Ƙaramar Hukumar Dánja, Jihar Kátsina A Darén Jiya Al-hamis

Tsaro
Ƴań Bìñďîģà Sun Sácé Mąhaifiýar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara A Gârin Kahutu Dáke Ƙaramar Hukumar Dánja, Jihar Kátsina A Darén Jiya Al-hamis Allah Ya Bayyana Ta Cikin Aminci. An baza jami'an tsaro na zuwa dazukan jihar Katsina dòmin su kubutar da mahaifiyar mawaƙi Dauda Rarara kamar yadda rundunar ƴansandan jihar Katsina ta bayyana Allàh ya bayyana ta. Ina Roƙon Ƴan Uwa Músúlm Da Ku Taya Ni Da Addu'ar Allâh Ya Kuɓutar Da Mahaifiyata, Ta Dawo Gida Cikin Ƙoshin Lafiya, Roƙon Mawaƙi Rarara Ga Al'ummar Nájeriya Allah Ya bayyana ta.
Yanzu-Yanzu: An kama wadanda suka Kàśhè janar din soja a Abuja, Kalli hotunansu

Yanzu-Yanzu: An kama wadanda suka Kàśhè janar din soja a Abuja, Kalli hotunansu

Tsaro
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, an kama 'yan fashin da suka kashe janar din soja mai ritaya a Abuja. An kama mutanen su 4 wanda aka bayyana sunayensu kamar haka: Ibrahim Rabiu, 33; Nafiu Jamil, 33; Aliyu Abdullahi, 47; Mohammed Nuhu, 28 Rahoto yace dukansu suna zaunene a Apo Primary school. Kuma duka sun amsa laifin da ake tuhumarsu dashi. Sunce aun kashe Brig.-Gen. Uwem Udokwere Ne bayan da suka ga ya fito da Bindiga yana shirin harbinsu. Kuma sun sace wayarsa da sauran wasu kayan amfani a gidan nasa. Ranar Asabar data gabata ne dai maharan suka yi wannan mummunar ta'asa wadda ta dauki hankula a Najeriya.
Hotuna: Jami’an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan àlbárusan bìndìga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan’musa a Jihar Katsina , tace yunwa ce tasa ta shiga wannan sana’a

Hotuna: Jami’an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan àlbárusan bìndìga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan’musa a Jihar Katsina , tace yunwa ce tasa ta shiga wannan sana’a

Tsaro
Hakika Maķàsañ Al'ummar Arewa Suna Tare Da Su Daga Bashir Babandi Gumel Jami'an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan albarusan bindiga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan'musa a Jihar Katsina kamar yadda ta bayyana yayin da Jami'an tsaron suke yi mata tambayoyi. Wannan kamu yana zuwa ne kwana daya da kaiwa wani mummunan harin ta'addanci a garin Maidabino dake karamar hukumar ta Danmusa wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 9 da kona motoci, gidaje, da satar kayakin masarufi da mutane sama da hamsin wadanda aka tafi dasu daji da sunan garkuwa dasu. Allah ka kawo mana karshen munafuka da masu yin zagon kasa ga harkokin tsaro da ke cikinmu tare da wannan masifa ta matsalolin tsaro da muke fama da su a yankin Arewa da kasa baki daya.
Matashi dan Najeriya yayi gàŕkùwa da kansa inda ya nemi mahaifinsa ya biya kudin fansa har dala $700,000

Matashi dan Najeriya yayi gàŕkùwa da kansa inda ya nemi mahaifinsa ya biya kudin fansa har dala $700,000

Tsaro
Wani matashi dan kimanin shekaru 20 a Legas yayi garkuwa da kansa inda ya nemi mahaifinsa ya biya kudin fansa har dala $700,000. Matashin shi da abokansa mata 4 sun kama gida ne suka boye a ciki inda yawa mahaifinsa karyar an yi garkuwa dashi. Saidai da bincike yayi tsanani an gano dabarar tasu. An kamasu ana kan bincike. Hukumar 'yansanda ta jihar Legas din ta tabbatar da lamarin da kama wanda ake zargi me suna Collins Ikwebe.
Tsananin Rashin Tausayi: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Tsananin Rashin Tausayi: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa an sace wata mata mai juna biyu mai suna Mrs Ogunbunmi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Majiyar mu ta rawaito cewa Matar wadda aka ce za ta haihu ta bar gidanta da ke Oke Lantoro zuwa babban asibitin jihar, Ijaiye dake Abeokuta,sai dai an yi garkuwa da ita a hanya. Mijinta, Ogunbunmi Lateef, ya ce ya samu sakon WhatsApp da ke sanar da shi sace matarsa. Kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi cikakken bayani ba. A cikin wata sanarwa da ta fitar, a ranar Alhamis, ta ce, “Wani Ogunbunmi Lateef na Oke Lantoro ya rawaito cewa matarsa mai juna biyu da za ta haihu ta bar gida zuwa Asibitin Jihar Ijaiye Abeokuta. Ogun na daya daga cikin jihar da ke fama da yawaitar laifuka a yankin Kudumaso Yamma. D...
Bidiyo da Hotuna Da Duminsu: Harin ‘Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata ‘Yan Sanda Biyu

Bidiyo da Hotuna Da Duminsu: Harin ‘Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata ‘Yan Sanda Biyu

Kano, Tsaro
Harin 'Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata 'Yan Sanda Biyu. Dama dai wasu na kokawa da cewa an jibge 'yan daba a fadar Sarkin Kano dake Kofar kudu inda wasu ke ganin hakan ka iya zama barazanar tsaro ga al'ummar dake kewaye da yankin. https://twitter.com/Musaddiqww/status/1803537550876815767?t=zFtVr6QilV2yJF7TI9xRQQ&s=19 An dai jawo hankalin jami'an tsaro kan wannan lamari: https://twitter.com/Musaddiqww/status/1803678430346530884?t=ARnpwjVzoX22x5VVfi-_sA&s=19 Jihar Kano dai ta kasance cikin rashin tabbas akan rikicin masarautar jihar tsakanin Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero.