Kwana nawa jinin haila yakeyi
Jinin Haila yanayin kwanaki 3 ne zuwa 8, amma da yawa jinin hailarsu yanayin kwanaki 5 Wanda hakan ba matsala bace.
Jinin yana zuba da yawa a kwanaki 2 na farko, sannan a kwanakin farko da kika fara jinin Al'ada, zaki iya ganin jini Pink, a yayin da ya kai kwanakin tsakiya, jinin zai iya komawa jaa, watau red, a yayin da yazo karshe, zai koma light Brown.
Idan kika gama jinin gaba daya, zaki ga farin ruwane kadai ke fita daga gabanki.
Idan kika yi kwanaki 90 ko watanni 3 baki ga jinin al'adarki ba kuma ba ciki kike dauke dashi ba, ba shayarwa kike ba, to ki gaggauta ganin likita.
Saidai akwai abubuwan dake sa kwanakin jinin al'adarki su canja ko su rikice:
Yawan shekaru: Mace data fara manyanta zata iya ganin kwanakin jinin al'adarta sun ragu kuma tana yawan yin jinin al'ada...