Kalaman barkwanci a soyayya
Kece Tabarmar baccina.
Dan wake da mai da yaji na.
Ina sonki kamar dan mangwaro idan yazo karshe.
Soyayyarki ta fi min rake zaki.
Da fari nasha tsikarina aka yi ashe soyayyarki ce ta sokeni.
Soyayyarki ta hanani ganin kyawun sauran mata.
Ko idona a rufe zan iya kai kaina gidanku.
Ko da mota, jirgin sama, Keke da babur sun daina aiki, zan iya yin tattaki daga Maiduguri zuwa Legas dan kawai in ganki.
Kin sace komai na jikina kin maye su da soyayyarki.
Bani da labari sai naki ko da cikin abokai da 'yan uwana.
Duk macen dana kalla, fuskarki kawai nake gani a jikinsu.
Kar ki jini shiru ni kaina na manta da kainane bayan zurfin da na yi a tunaninki.
Zan iya shan shayi ba madara ba suga, zan iya cin abinci ba yaji ba miya ko gishiri muddin kece zaki bani.
Za...