Yadda Yaro Ya Jagoranci Ķìsàn Mai Gidanśa Tare Da Ƙòñe Gawar Šà À Kano
Daga Anas Saminu Ja'en
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu Matasa Uku da suka haɗar da Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam da kuma Sadik Sunusi da ake zargin su da kisan wani Matashi Dahiru Musa me shekaru 32 a Unguwar Gaida ƴan Kusa, bayan sun gayyace shi har gida suka ba shi shinkafar bera a cikin abinci, tare da caççaka masa wuka har ya mutu daga ƙarshe suka bankawa gawàŕ sa wuta.
Kakakin rundunar ƴan Sanda SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Ya wallafa Labarin.
YADDA ABUN YA KASANCE: Wani ɗan uwan sa da muka sakaye sunan sa, Ya bayyana wa Anas Saminu Ja'en abun da ya faru da Matashin Dahiru Musa wato Alh. Senior mai kimanin shekaru 33 mazaunin Layin Gidan Tsamiya da ke Ɗorayi Gidan Dakali a jihar Kano, Ya ce a ranar Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024 Marigayi Baba Alhaji bai kwana...