Monday, January 13
Shadow

Amfanin Kanunfari

Kanunfari yana maganin sanyi

Amfanin Kanunfari
Tabbas Kanunfari yana maganin sanyi kamar yanda masana ilimin kiwon lafiya suka tabbatar. A mafi yawancin lokuta akan hada Kanunfari da zuma ne dan samun sakamakon maganin sanyi me kyau. Masana sun bayyana hadin Kanunfari da zuma a matsayin na gaba-gaba wajan magance matsalar sanyi da mura. A yayin da mutum ke fama da kaikayin makogoro, shima wannan hadi na da tasirin da zai magance wannan matsalar. Yanda ake hadin shine: Za'a samu Kanunfari kamar kwaya 6 a dan dorasu a wuta a dan gasa. Sannan a daka su su zama gari. Sai a zuba babban cokali na zuma a ciki. Ana shan wannan hadi sau biyu zuwa uku a kullun dan maganin tari mura da kaikayin makogoro.

Kanunfari yana maganin infection

Amfanin Kanunfari
Eh! Kanunfari yana maganin infection. Bincike ya tabbatar da cewa, man Kanunfari na dauke da sunadaran Antibacterial, Antifungal, Insecticidal, da kuma Antioxidant. Dan haka masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, Kanunfari yana taimakawa wajan rage ciwon lokacin al'adar mata hakanan kuma yana maganin Infection. Kanunfari, musamman manshi yana maganin infection na al'aura ko farjin mata, matsaloli irinsu kaikan gaban mace, zafin gaban mace ko fitar da ruwa. Ana iya samun man Kanunfari a kasuwa ko kuma ana iya hadashi a gida. Yanda ake hada man Kanunfari a gida shine, ana samun Kanunfarin a daka a zuba a wata roba ko kwalba, sannan sai a samu man zaitun, kwa-kwa ko wani a zuba a ciki. Sai a kulle wannan kwalba ko roba zuwa sati daya. Bayannan sai a samu rariya a ta...

Kanunfari da zuma

Amfanin Kanunfari
Hadin Kanunfari da zuma na da matukar amfani a jikin dan Adam daya daga ciki shine idan akwai matsalar ciwon makoro. Shan wannan hadi yana taimakawa sosai wajan magance matsalar makogoro. Hakanan wannan hadi yana da matukar amfani ga masu fama da mura da tari, musamman lokacin sanyi. Hakanan wannan hadi na karawa garkuwar jikin mutum karfi sosai. Wannan hadi kuma yana taimakawa wajan magance matsalar warin baki da sauran matsalolin cikin bakin.

Amfanin kanunfari da madara

Amfanin Kanunfari
Amfanin hadin Kanunfari da madara na da yawa sosai. Daya daga ciki shine yana taimakawa sosai wajan magance matsalar warin baki ko kuma hana narkewar abinci ko a ce bata ciki. Wannan hadi kuma na Kanunfari da Madara yana kawar da Kasala. Hakan kuma yana taimakawa wajan daukar ciki. Ga wanda basu da karfin jima'i, yana taimakawa sosai wajan karawa namiji kuzari. Yana kara karfin Garkuwar jiki. Yana kuma karawa kashin mutum karfi sosai. Yana kashe Bacteria. Yana maganin kansa, watau ciwon daji, musamman na mama ga mata. Yana kuma taimakawa karfin ido wajan gani. Ga mai fama da sarkewar Numfashi, ko numfashi sama-sama, Kanunfari da Madara na taimakawa wajan magance wannan matsala. Yana kuma karawa namiji yawan maniyyi da karfin fitar ruwan maniyyin.

Amfanin kanunfari ga budurwa

Amfanin Kanunfari
Kanumfari yana da matukar Amfani ga Budurwa dama sauran mata gaba daya. Da farko dai ana amfani da Kanunfari wajan magance matsalar ciwon mara da sauran ciwukan da ake ji a lokacin Al'adar mata. Hakanan Kanunfari yana kuma taimakawa sosai wajan magance matsalar ciwon daji na mama, watau Breast cancer da mata ke fama dashi. Hakanan Kanunfari yana maganin kurajen fuska sosai. Yana kuma hana tattarewar fata yanda fata zata zama kamar ta matashiya. Hakanan Mata na iya amfani da Kanunfari wajan karawa kansu ni'ima da kuma samun gamsuwa yayin jima'i. Yanda mata zasu hada Kanumfari dan amfaninsu: Dan Magance matsalar ciwon mara da sauransu lokacin al'ada, mata na iya hada shayin Kanunfari a rika sha kadan-kadan. Hakanan dan magance matsalar kurajen fuska ko magance matsalar t...

Amfanin shan ruwan kanunfari ga maza

Amfanin Kanunfari
Maza na iya Amfani da ruwan Kanunfari a matsayin shayi a rika sha. Amfanin hakan shine yana karawa namiji karfin Azzakari sosai. Sannan ga wanda yake da matsalar rashin mikewar Azzakari, zai iya amfani da ruwan kanunfari wajan magance matsalar. Wanda kuma yake son kara karfin sha'awarsa, shima yana iya amfani da ruwan kanunfari wajan hakan. Saidai masana kiwon lafiya sun bada shawarar a rika shan ruwan Kanunfari ba da yawa ba dan kar ya zama illa ga maisha maimakon amfanarwa.

Amfanin man kanunfari ga azzakari

Amfanin Kanunfari, Kiwon Lafiya
Man Kanunfari an dade ana amfani dashi wajan magance matsalar rashin kuzarin namiji wajan jima'i. Yana kara karfin Azzakari kuma yana karawa namiji kuzari wajan gamsar da mace a gado. Idan mutum na fama da matsalar kawowa da wuri yayin saduwa da iyali, ana amfani da Kanumfari wajan magance wannan matsala. Hakanan idan mazakutar mutum bata mikewa, shima Kanunfari yana taimakawa sosai wajan magance wannan matsala. Idan mutum yana son karfin sha'awarsa ta karu, to yana iya amfani da Kanunfari wajan karawa kansa karfin sha'awa. Yawanci amfanin Kanunfari yana bangaren kara karfin Azzakarine da kuma karawa namiji kokari sosai wajan gamsar da iyalinsa. Hanyoyin da ake amfani da Kanunfani sune: Ana iya mayar dashi gari, kamar na yaji ko a hadashi da yaji a rika barbasawa a abi...