Tafarnuwa na maganin infection
Infection na mata da suke fama dashi a gabansu abu ne wanda ya zama ruwan dare, a wani binciken masa na jami'ar Harvard sun bayyana cewa kaso 75 cikin 100 na mata sun taba samun ko kuma zasu samu cutar Infection a rayuwarsu.
Tafarnuwa na taimakawa sosai wajan magance matsalar cutar Infection tana hana abinda ke zama a farjin mace ya bata infection yaduwa.
Infection din gaban mata ana kiransa da Yeast infection a turance, shi Yeast din wani ruwa ne da a gaban kowace mace akwaishi, amma akan samu matsala wani lokacin sai yayi yawa sosai shine sai ya koma ya zama infection.
Ga alamomin da mace zata gane tana da cutar Infection kamar haka:
Idan kika ji gabanki na kaikai ko yana miki ba dadi.
Idan kina jin zafi yayin jima'i.
Idan farin ruwa me kauri na fita daga gabanki.
A...