Tuesday, January 14
Shadow

Kiwon Lafiya

Ciwon kirji gefen hagu

Ciwon Kirji
Ciwon kirji a gefen hagu na iya kasancewa alama ta matsaloli daban-daban, kuma wasu daga cikin waɗannan matsalolin suna iya buƙatar kulawa ta gaggawa. Ga wasu daga cikin mafi yawan abubuwan da ke haifar da ciwon kirji a gefen hagu da kuma alamominsu: Abubuwan da Ke Haifar da Ciwon Kirji a Gefen Hagu 1. Ciwon Zuciya (Angina) Alamomi: Jin ciwon kirji mai nauyi ko matsin lamba a gefen hagu, wanda zai iya bazuwa zuwa wuyan hannu, wuya, ko jaw. Yana iya zama da wahalar numfashi da zufa. Abin Yi: Nemi taimakon likita da gaggawa. 2. Harbin Zuciya (Heart Attack) Alamomi: Jin zafi mai tsanani ko matsin lamba a tsakiyar kirji ko gefen hagu, wanda zai iya bazuwa zuwa wuyan hannu, bayansa, wuya, ko jaw. Yana iya zama tare da zufa, jiri, wahalar numfashi, ko jin amai. Abin Y...

Alamomin ciwon kirji

Ciwon Kirji
Ciwon kirji yana iya kasancewa alama ta matsaloli daban-daban, wasu daga ciki suna bukatar kulawar gaggawa. Ga wasu daga cikin alamomin ciwon kirji da kuma wasu daga cikin cututtukan da suke iya haifar da ciwon kirji: Alamomin Ciwon Kirji Jin nauyi ko matsin lamba: Jin nauyi, matsin lamba ko ƙunci a tsakiyar kirji na iya zama alamar matsala mai tsanani kamar ciwon zuciya. Ciwon da ya bazu: Ciwon da ya bazu zuwa hannuwa (musamman hagu), wuyan hannu, bayansa, wuyansa, haba, ko ciki. Rashin numfashi: Jin wahalar numfashi ko numfashi mai tsanani. Daukewar numfashi: Jin cewa numfashi na ɗaukewa yayin aikata wani abu ko bayan an gama wani aiki. Yawan zufa: Yawan zufa da ba za a iya bayyana ba. Jin jiri ko raunana: Jin jiri, raunana, ko kamar za a suma. Nauyin zuciya ...

Alamomin ciwon damuwa

Kiwon Lafiya
Alamomin ciwon damuwa (depression) na iya bambanta daga mutum zuwa mutum, amma ga wasu daga cikin mafi yawan alamomi: Rashin jin dadin rai ko jin bakin ciki: Mutum na iya jin baƙin ciki ko rashin jin daɗi na tsawon lokaci. Rashin sha’awar abubuwan da suka saba ba shi daɗi: Mutum na iya daina jin daɗin abubuwan da suka saba ba shi daɗi, kamar ayyukan yau da kullum ko dangoginsa. Rashin karfi ko gajiya: Jin gajiya ko rashin kuzari duk da ba a yi wani aiki mai wahala ba. Canje-canje a yanayin barci: Rashin iya yin barci ko yin barci fiye da kima. Canje-canje a yanayin cin abinci: Rashin sha’awar cin abinci ko yawan cin abinci fiye da kima, wanda zai iya haifar da asarar nauyi ko karin nauyi. Tunanin kashe kai ko kisa: Tunanin ko kiran son kashe kansa ko yin kisa. Rashin ...

Alamomin hawan jini

Duk Labarai, Hawan Jini
A mafi yawan lokuta, hawan jini baya nuna wata alama da zata tabbatar mutum ya kamu dashi. Saidai yana kara hadarin kamuwa da cutar zuciya, Shanyewar rabin jiki, da sauran matsaloli masu yawa. Menene Hawan Jini? Hawan Jini yana nufin idan jinin mutum ya taru yayi yawa fiye da yanda ya kamata, wanda hakan zai sa Zuciyar mutum ta yi aiki fiye da yanda ya kamata. Hawan jini, wanda aka fi sani da "high blood pressure" a Turance, yanayi ne da ake samun karuwar matsa lamba na jini a jikin mutum. Wannan yanayi na iya zama mai hadari domin yana iya haifar da matsaloli masu yawa kamar su bugun zuciya, bugun jini (stroke), da sauran matsalolin lafiyar zuciya. Ana auna hawan jini ta hanyar amfani da lambobi biyu, wanda ake kira systolic (lambobin farko) da diastolic (lambobin ƙarshe)...

Alamomin ciwon zuciya ga mata

Ciwon Zuciya
Ciwon zuciya na daya daga cikin abubuwan dake kashe mata da maza. Alamomin ciwon zuciya kusa dayane ga duka mata da maza. Ga alamomin ciwon zuciya ga mata kamar haka: Ciwon wuya, haba, kafada, baya, da saman ciki. Sarkewar Numfashi. Jin ciwo a daya ko duka hannuwa. Yawan ciwo da safe da amai. Zufa. Jin kanki ba nauyi da Juwa. Jin Kasala sosai. Zafin Zuciya. Abubuwan da ka iya sa ciwon zuciya ya tsananta a jiki mata: Ciwon Suga: Duk macen dake fama da ciwon sugar na cikin hadarin iya kamuwa da ciwon zuciya. Damuwa da Kunci: Matsalar damuwa da kunci ta fi baiwa mata alamun kamuwa da cizon zuciya fiye da maza. Shan Taba ko Wiwi:Mace me shan taba ko wiwi tafi maza zama cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya fiye da maza. Rashin Motsa jiki: Yawan zam...

Maganin bugawar zuciya da sauri

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Bugawar zuciya da sauri na iya faruwa a kowane lokaci kuma abune wanda ke zuwa ya wuce, akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan Maganin bugawar zuciya da sauri. Ga abubuwan dake kawo bugawar zuciya da sauri kamar haka: Motsa jiki. Kishirwa me tsanani. Rashin Lafiya. Shiga halin takura. Me ciki na iya fuskantar hakan. Shaye-shayen miyagun kwayoyi. Shan taba Wasu daga cikin maganin bugawar zuciya da sauri sune: Tashin Hankali:Tayar da hankali na sa bugawar zuciya da sauri, dan haka neman maganin kwanciyar hankali da samun nustuwa zai taimaka magance wannan matsalar. Hanya ta gaba wajan magance matsalar bugawar zuciya da sauri itace a kwanta a kan gadon baya ko kuma ace rigingine sai a rika yin kamar ana tari, a dan rike numfashi sai a sakeshi. Ana k...

Maganin ciwon zuciya na Gargajiya

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Ciwon zuciya wanda yayi tsanani yana bukatar kulawar kwararren likita, saidai idan bai yi tsanani ba, ana iya amfani da magungunan gargajiya wajan maganceta Irin ciwon zuciyar da ake magancewa a gida shine wanda baya faruwa a kullun, watau na dan lokacine, sai kuma damuwa, da daurewar gabobi, sai da yawan gyatsa. Wasu lokutan akwai wahala wajan gane ko banbance kalar ciwon zuciyar da ya kamata a magance a gida da wanda ya kamata aje Asibiti. Idan aka ji wadannan alamu na kasa to a je Asibiti: Ciwin kirji idan ya yi tsanani yana daurewa, yayi nauyi ko yana nusar mutum. Idan mutum ya ji kamar zuciyarsa zata buga. Idan aka ji alamar numfashi na neman daukewa. Idan ba'a ji wadannan alamu na sama ba to za'a iya gwada maganin gargajiya na gida kamar haka: Ana iya samun ts...

Ana warkewa daga ciwon zuciya

Ciwon Zuciya
Ya danganta da irin ciwon zuciyar daya kamaku, mun yi bayani akan kalolin ciwon zuciya da ake dasu, Alamomin ciwon zuciya Idan ciwon zuciyar Coronary artery disease ne ya kamaka, maganar gaskiya ta masana kiwon lafiya sun ce ba'a warkewa daga kalar wannan ciwon zuciya. Yanda zaka san kalar ciwon zuciyar da ya kamaka shine ka yi magana da likitanka ko kuma ka karanta takardar sakamakon gwajin da aka maka. Da zarar likitoci sun tabbatar da cewa wannan kalar ciwon zuciyar ne kake dashi to bai da magani, saidai akwai hanyoyin da ake bi dan kada wasu sauran matsaloli irinsu bugun zuciyar farat daya ya kama mutum. Masana sun ce idan irin wannan ciwon zuciya ya kamaka, yana da kyau ka rika kula da cin abinci me gina jiki, ba komai zaka rika ci ba. Motsa jiki akai-akai shima yana ta...

Alamomin ciwon zuciya

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Ciwon zuciya ya danganta da irin zuciyar, akwaishi kala-kala. Dan haka bari mu bayyana alamomin ciwon zuciya daban-daban. Akwai wanda ake kira da Coronary artery disease: Wannan kalar ciwon zuciya ne dake taba hanyoyin dake baiwa zuciyar jini. Wannan kalar ciwon zuciya shine wanda yafi kama mutane kuma yakan kai ga Bugawar Zuciya da ke iya kaiwa ga mutuwa, Yakan kuma kai ga ciwon kirji, ko shanyewar rabin jiki. Alamomin wannan ciwon zuciya ya banbanta a tsakanin mata da maza, misali, idan ya kama maza, zasu iya fuskantar ciwon kirji, yayin da idan ya kama mata, zasu iya fuskar Ciwon kirjin da karin wasu matsaloli da suka hada da numfashi sama-sama, da yawan zazzabi da safe da kuma matsananciyar kasala. Ga dai alamomin ciwon zuciya na Coronary artery disease dake damun maza d...

Kumburin kafa ga mai ciki

Haihuwa, Laulayin ciki
Mai ciki zata yi fama da kumburin kafa, musamman idan cikin ya fara girma. Hakan na faruwane saboda nauyin abinda ke cikinta. Hakan nasa jini ya rage gudana a kafarki, Musamman idan ana yanayim zafi ko kuma kin dade a tsaye. Bayan girman da abinda ke cikinki yake yi, a yayin da kike da ciki, yawan ruwan dake jikinki yana karuwa. Hakan kuma nasa ciwon kafa. Kafa da gwiwoyinki da tafin kafa da yatsu duk zasu iya kumbura. Yayin da cikinki ke kara girma, kumburin shima zai rika karuwa a hankali. Saidai wannan kumburi idan dai ba ya wuce lissafi ba, bashi da cutarwa ga Mahaifiya ko abinda ke cikinta. Alamomin dake nuna kumburin me ciki me cutarwane kuma yana bukatar kukawar likita Idan lokaci guda kumburin ya karu a fuska, hannu da tafin kafa. Idan ciwon kai me tsa...