Siffofin mace mai ciki
Mace me ciki na da siffofin da ake gane ta dasu kamar haka.
Wata na yi katon ciki, Musamman me 'yan biyu ko 'yan uku, ana ganinta da katon ciki.
Kamanninta zasu canja, Mafi yawa zaka ga kamannin me ciki sun canja, fuskarta ta ciko sosai.
Yawan tofar da yawu, wata Mace me ciki takan rika tifar da yawu saboda rashin dandano da take ji a bakinta.
Nishi: Wata mace me cikin takan rika yin nishi saboda laulayin cikin da take dauke dashi.
Canjawar dabi'a: Wasu dabi'unsu na canjawa inda zaka ga wasu har duka suna yi.
Yanda ita kanta mace zata gane tana da ciki:
Zubar da jini wanda bana al'ada ba.
Kan nono zai rika zafi, zai ya kumbura.
Kasala.
Ciwon Kai.
Amai.
Rashin son cin abinci.
Yawan Fitsari.
Babbat hanyar da ake gane mace na da ciki shine a yi gwaji...