Friday, December 13
Shadow

Nawa ne farashin dala a yau

Darajar Naira ta tashi sosai a kasuwar Canji: Farashin dala a yau

Darajar Naira ta tashi sosai a kasuwar Canji: Farashin dala a yau

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta tashi sosai a kasuwar canji a yau Talata, 8 ga watan October. A yau din an sayi dala akan naira 1561.76 a ranar Litinin dai an sayi dalar akan Naira N1635.15 hakan na nuna Naira ta samu karuwar daraja har ta Naira 73.39. Hakan ya farune a kasuwar Gwamnati. Saidai a kasuwar bayan fage, Darajar Nairar faduwa ta yi inda aka sayi dala akan Naira 1780.
Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar Chanji inda aka sayi dala akan Naira 1,575

Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar Chanji inda aka sayi dala akan Naira 1,575

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar bayan fage ta 'yan Chanji indaka sayi dalar Amurka akan Naira 1,575 a ranar Laraba. A ranar Talata dai an sayi dalar ne akan Naira 1,565. Hakanan a kasuwar gwamnati ma Darajar Nairar kara kasa ta yi inda aka sayi dala akan Naira 1,586.71. Hauhawar farashin dala dai na daya daga cikin abubuwan da ake alakantawa da hauhawar farashin kayan masarufi. Musamman lura da cewa mafi yawan kayan amfani aana shigo dasu Najeriya ne daga kasashen waje.
Nawane Farashin dala a yau, 31/05/2024, Darajar Naira ta fadi

Nawane Farashin dala a yau, 31/05/2024, Darajar Naira ta fadi

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta fadi a kasuwar canji ta gwamnati a jiya, Alhamis. Kwanaki 3 kenan a jere darajar Nairar na faduwa a kasuwar Gwamnati. A jiyan, an sayi dalar Amurka akan Naira N1,484.76 wanda hakan ke nuna Naira ta samu faduwar 145.2 idan aka kwatanta da farashin ranar Laraba na Naira N1329.65 akan kowace dala. Saidai a kasuwar 'yan Chanji, Nairar ta dan samu tagomashi na Naira 5, inda aka sayi dalar akan Naira N1,485.
Nawane farashin dala a yau 30/05/2024: Naira ta farfado

Nawane farashin dala a yau 30/05/2024: Naira ta farfado

Nawa ne farashin dala a yau
Farashin Naira a kasuwar 'yan canji ta dan farfado a ranar Laraba, 29/05/2024. An sayi dalar Amurka akan Naira 1,375, idan aka kwatanta da farashin da aka sayi dalar ranar Talata watau Naira 1,500, za'a iya cewa farashin Nairar ya farfado. Saidai kuma a kasuwar Gwamnati, farashin Nairar faduwa yayi inda aka sayi dala akan Naira, 1,339.33. Tashi da faruwar Dala dai na daya daga cikin abubuwan dake ciwa Najeriya tuwo a kwarya.
Nawane farashin Dala a yau, 29/05/2024

Nawane farashin Dala a yau, 29/05/2024

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta dan fara dawowa inda a jiya, Talata aka sayi dalar Amurka akan Naira 1,173 a farashin Gwamnati. A ranar Litinin dai an sayi dalar akan Naira 1,500 ne a farashin Gwamnatin. Shi kuwa farashin Pound an saye shine akan Naira 1,888, sai kuma Euro da aka siya akan Naira 1,630. An sayi dalar Canada akan Naira 1,112. Sai kuma kudin China, Yuan an sayeshi akan Naira 150.