
A yayin da a dazu muka kawo muku cewa, Davido ya saka kalaman da Rarara ya masa, a shafinsa na X.
Inda ya rubuta cewa, Rararan ko sunansa bai iya fada ba, Debidoo yake cewa.
A yanzu Davido yayiwa Rarara martani da Hausa.
Ya wallafa a Story dinsa na Instagram cewa, Rarara ya kamata ya zama dan kishin kasa sannan ya daina fifita son ransa akan abinda ya shafi al’umma.
Sannan ya daina zama karan farautar ‘yan siyasa.
Yace kuma duk mutum me kishin kasa ba zai yi shiru akan abinda ke faruwa a Najeriya ba.
Davido ya kara da cewa, da ace kana da Ilimi da na tsaya na yi magana da kai, amma komai baka sani ba sakarai kawai.

