
Rahotanni daga jihar Kani na cewa, an samu baraka a jam’iyyar NDC.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Hon. Hussaini Isah Mairiga bisa ga hadin gwiwar shugaban jam’iyyar na kasa, Seriake Dickson ne suka fitar da sabon tsarin raba mukaman ‘yan takarar jam’iyyar Inda aka baiwa Kwankwasiyya kaso 60, aka baiwa sauran bangarori kaso 40.
A cewarsu, haka ne alkawarin da aka yi ba yanda a yanzu Kwankwasiyya ta dauke duk wani mukamin takara a jihar ba.
Saidai Rahotanni sun ce Kwankwaso yayi barazanar ficewa daga jam’iyyar muddin aka ce za’a yi amfani da wannan tsarin.
canje-canjen sa aka yi sune kamar haka:
- Barrister Isma’il Idris Sani – Kumbotso
- Nasiru Ali Ahmed – Nassarawa
- Kabiru Ishaq Sa’id – Kano Municipal
- Barrister Dayyabu Jamilu Ibrahim – Doguwa/Tudun Wada
- Muhammad Hamisu Abubakar – Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa
- Ibrahim Bashir Bango – Sumaila/Takai
- Abdulmajid Isa Umar Mairigar Fata – Gwale
Hakanan an canja ‘yan takara a mazabun jiha Dala, Tarauni, Kumbotso, Ungogo, da Dawakin Kudu