Friday, April 10
Shadow

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: A yau Sallah, Daya daga cikin iyalin malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta rigamu gidan gaskiya yayin da yake tsare a hannun ICPC

Rahotanni sun bayyana cewa, a yau Sallah, Matar Marigayi yaya a wajan tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, watau Bashir ElRufai, me suna Hajiya Safiya Ali Rufai ta rigamu gidan gaskiya.

Ta rasu ne bayan gajeruwar rashin Lafiya.

Dan tsohon Gwamnan, Hon. Bello ElRufai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X.

Da fatan Allah ya jikanta.

Karanta Wannan  RAN MAZA YA ƁACE: Shugaban Hafson Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya sauka jihar Borno, don ƙarfafa wa dakarun Sojin Nijeriya gwiwa, biyo bayan yawaitar hare-haren 'yan tà'àddà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *