
Wani jigo a Jam’iyyar APC me mulki, Tolu Bankole wanda yana cikin kwamitin gudanarwa na Jam’iyyar ya bayyana cewa babu gurbi a Aso Rock sai shekarar 2031 bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala wa’adinsa na mulki.
Ya bayyana cewa, shugaba Tinubu ba zai sauka daga mulki ba sai ya cika wa’adin da kundin tsarin mulki ya bashi damar yi na shekaru 8.
Da yake magana akan hadaka da ake samu tsakanin ‘yan adawa da niyyar kayar da gwamnatin Tinubu a shekarar 2027, yace yana baiwa ‘yan adawar shawarar dama kada su bata kudadensu da lokutansu.
Yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi ayyuka da suka amfani mutane sosai sannan suka habaka tattalin arzikin Najeriya.