
Biyo bayan kashe Salwan Momika da ya kona Qur’ani a bainar jama’a, an sake samun wasu da yawa sun sake kona Qur’anin inda suka rika saka hotunan wannan lamari a shafukansu na sada zumunta.
Wani me sunan DigitalVagrant a kafafen sada zumunta ya bayyana cewa, zai maye gurbin Salwan Momika inda ya fita fili ya kona Qur’ani a Manchester dake kasar Ingila.
Tuni dai mahukunta a birnin suka kamashi saboda yunkurin kawo fitina.
Akwai da yawa da ake samu suna cin zarafin addinin Musulunci ta hanyoyi daban-daban dan tsananin nuna kiyayya.