Monday, June 29
Shadow

Kalli Bidiyon: A karshe dai, Aminu Warkal ya bayyana laifin da matarsa ta mai ya saketa

Bayan da matarsa ta fito kafafen sada zumunta ta bayyana cewa ya saketa tsakar dare ya kuma ce ta fitar masa daga gida, Aminu Warkal ya bayyana dalilin da yasa ya mata hakan.

A martaninsa, Aminu Warkal yace matarsa da suna zaune lafiya, kawai sai ta fito da wani sabon hali na rashin godiya kan dukkan abinda ya mata.

Yace sannan babu wata magana me dadi dake shiga tsakaninsu.

Yace hakanne da abu yayi kamari shine suka rabu.

Yace babban abinda ya kawo rabuwar shine dabbobinsa da ta dauka ta sayar ba da izininsa ba, sannan ya kulle mata gida yace ta je ta dawo dasu amma taki.

Karanta Wannan  Ance Maulidin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ake yi to me ya kawo hoton Sheikh Inyas a rigunan masu maulidin, sannan Mun fito zamu shago an rufe mana hanya, me yasa ba za'a iya yin Maulidin a gida ba sai an rufewa mutane hanya? Rukayya ta tambaya

Saidai yace duk da wannan abu da ya faru tsakaninsu, har yanzu da zata kirashi tace yayi hakuri, da zai mayar da ita dakinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *