
A yayin da suke ci gaba da shagalin Bikinsu, Peller da Jarvis shahararrun ‘yan Tiktok na kudancin Najeriya sun dauki hankula.
A wajan daya daga cikin bukukuwan nasu an ji an saka wakar mawakin Najeriya, Garzali Miko.
Lamarin ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda ake ta masa murna.
Garzalin da kansa ya wallafa Bidiyon wakar tasa da aka saka a wajan Bikin inda yake nuna godiya.
Wasu dai na cewa da Alama Garzali ya hakura ma da waka amma a yanzu gashi ya fara samun daukaka.