
Wannan wata matar aure ce da ta dauki hankula a kafafen sada zumunta saboda yanda ta bayyana cewa ta baiwa mijinta yadda dari bisa dari.
Matar tace ko a cikin mata aka ce mata an ga mijinta ko an ganshi a gidan Qaruwai tasan ta yadda dashi ba zai ci amanarta ba.
Ta bayyana cewa tana baiwa mata shawarar su rika baiwa mazansu yadda ko da kuwa sun san cewa suna neman mata, hakan zai sa su rika jin kunyar matan nasu, sannan watakila dalilin hakan yasa su shiryu.