Kalli Bidiyon: Yanda Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa, Sule Garo suka je fadar Sarkin Kano aka yi zikirin shekara dasu
by Bashir Ahmed
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Murtala Sule Garo sun je fadar Sarkin Kano, Me martaba Muhammad Sanusi II inda aka yi zikirin shekara dasu.
Sannan an yiwa Najeriya Addu’ar ci gaba da zaman lafiya a wajan.
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, HE Abba Kabir Yusuf, tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, HE Abba Kabir Yusuf, tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, sun halarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, PhD, CON, a yau Juma’a yayin gudanar da Zikirin Shekara da addu’o’in neman zaman lafiya ga ƙasa baki ɗaya. Taron ya haɗa manyan baƙi, malamai, masu riƙe da sarautu, da ɗimbin al’umma, inda aka roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ci gaba da wanzar da zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban Najeriya. Allah Ya ci gaba da kare ƙasarmu, Ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa. Amin., sun halarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, PhD, CON, a yau Juma’a yayin gudanar da Zikirin Shekara da addu’o’in neman zaman lafiya ga ƙasa baki ɗaya. Taron ya haɗa manyan baƙi, malamai, masu riƙe da sarautu, da ɗimbin al’umma, inda aka roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ci gaba da wanzar da zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban Najeriya. Allah Ya ci gaba da kare ƙasarmu, Ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa. Amin.