
Rahotanni sun bayyana cewa, ma’aikatan hukumar KNUPDA dake kula da gidaje a Kano sun tsere daga ofisoshinsu bayan kisan mutane 4 a Rimin Auzinawa, Ungoggo, Jihar Kano.
Gidaje kusan 40 ne aka sakawa fentin rusau.
Jaridar Daily Trust tace ta kai ziyara hukumar dan tattaunawa da jami’anta dan jin ba’asin yanda lamarin ya faru amma bata iske kowa ba sai ma’ikaci daya.
Kuma ya shaidawa jaridar cewa, tsoron kawowa hukumar harine yasa ma’aikatan hukumar suka tsere suka dauke motoci da sauran ababen hawansu.
Jaridar ta Daily Trust ta kuma kara ruwaito cewa, jami’in hukumar ta KNUPDA ya shaida mata cewa, ba sune suka je suka yi wancan rusau din ba da ya jawo asarar rayuka.