Wednesday, August 19
Shadow

Kalli Bidiyon: Yanda matar tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke rokon shugaba Tinubu, Kai Uba ne ga kowa dan Allah a sassautawa mijina sharudan beli saboda sharudan da aka saka masa yanzu ba zai iya cika su ba

Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Asiya Nasiru El-Rufai da kishiyarta, Aichatou sun kira taron manema labarai inda a ciki suka roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya taimaka ya saka baki a maganar shari’ar mijinsu.

Tace babu lungu da sakon da bata shiga ba a Kaduna tawa Shugaba Tinubu yakin neman zabe sannan kuma shima mijinta ya masa yakin neman zabe.

Tace ba wai sun ce kada a hukunta mijin nasu ba amma a bashi hakkokin da doka tace a bashi na ganin likitansa da bayar da belinsa.

Tace suna neman a sassauta sharudan belin da aka gindaya masa inda tace wanda aka saka masa yanzu sun yi tsauri ba zai iya cikasu ba.

Karanta Wannan  An ɗage taron mahaddata Qur'ani da aka shirya yi a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *