Sunday, March 23
Shadow

Bìndìgù Sama da Dubu uku sun bace a hannun ‘yansandan Najeriya

Majalisar tarayya ta tuhumi shugaban ‘yansandan Najeriya, (IGP),  Kayode Egbetokun bisa bacewar Bindigu 3,907 a hannun ‘yansandan.

Hakanan an masa tambayoyi game da aikata ba daidai ba da kudi a shekarar 2019.

Shugaban ‘yansandan da farko ya baiwa majalisar hakuri kan rashin amsa gayyatar da suka masa.

Sannan ya wakilta mataimakinsa, AIG Suleiman Abdul ya wa ‘yan majalisar jawabi kan tambayoyin batan kudaden da suke masa.

Saida ya kasa bayar da gamsashshiyar amsa game da bacewar Bindigun inda suka nemi a shiga tattaunawar sirri a kori ‘yan jarida daga dakin taron.

Saidai ‘yan majalisar sun ki amincewa da wannan kira inda suka ce shugaban ‘yansandan ya kkma ya nemo amsar tambayoyin da suka masa.

Karanta Wannan  'Hotuna Da Duminsu: Yansanda sun harbawa masu zanga-zangar goyon bayan sanata Natasha Akpoti barkonon tsohuwa a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *