
Kamfanin kere-kere na sojojin Najeriya, DICON ya bayyana Bindigar yaki ta farko da ya kera.

Kamfanin ya bayyana hakane a matsayin ci gaba da kuma rage dogaro da kasashen waje waja samar da makamai.
Masu sharhi na bangaren tsaro sun bayyana cewa, wannan ba karamin ci gaba bane.

‘yan Najeriya da yawa sun bayyana farin ciki da wannan labari inda suka ce ya kamata a samar da Bindigar da yawa ta yanda sojoji zau rika amfani da ita wajan yaki.