Friday, February 7
Shadow

APC ta kori ministan Buhari, Aregbesola

Jam’iyyar APC ta kori tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan cikin gida Rauf Aregbesola, a kan zarginsa da yin abubuwan da suka saba wa jam’iyyar.

Reshen jam’iyyar na jihar ta Osun shi ne ya tabbatar da korar a wata wasika da ya fitar.

Aregbesola, wanda ya kasance ministan cikin gida a lokacin gwamnatin da ta gabata, ya jagoranci wani bangare na jam’iyyar ta APC a jihar, bangaren da aka yi wa lakabi da “The Osun Progressives,” wanda kuma daga baya aka sake masa lakabi da ”Omoluabi Caucus”.

Korar tsohon gwamnan ta biyo bayan taron da bangaren da yake jagoranta ne wato Omoluabi Caucus, ya gudanar kuma karkashin jagorancin, Aregbesola.

Karanta Wannan  Kuma Dai: Kwanaki kadan bayan da EFCC ta kori jami'anta daga aiki saboda cin hanci da rashawa, Dala $400,000 da Gwalagwalai na miliyoyin Naira sun bace a ofishin EFCC din

A lokacin taron bangaren ya sanar da aniyarsa ta ficewa daga APC,inda ya bayar da hujjar raguwar tasirin jam’iyyar a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *