
Wata daliba a jami’ar Nnamdi Azikiwe University dake Awka jihar Anambra ta mari malaminta sannan ta cijeshi.
Dalibar dai tana daukar bidiyon Tiktok ne sai malamin ya zo wucewa ya mata magana tare da dan tureta.
Saidai ta juya ta rika zaginsa da gaya masa kalamai marasa dadi inda shi kuma ya nemi ta goge bidiyon da ta dauka.
Saidai ta ki inda ta cukumeshi ta mareshi ta kuma cijeshi, a karshe dai da kyar aka kwaceshi a hannunta inda sai da aka kaishi asibiti.
Tuni dai makarantar ta sanar da cewa ta dauki matakin yin bincike akan lamarin kamin tasan hukuncin da zata yanke.