
Rahotanni sun bayyana cewa, Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle zai aurar da ‘ya’yansa maza da mata su 9.
Katin gayyatar auren ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga cewa za’a yishi ne ranar 6 ga watan Fabrairu a babban masallacin Juma’a dake Abuja.
Sunayen ‘ya’yan nasa sune kamar haka, Ibrahim, Suraj, Safiya, Maryam, Aisha, Fahad, Muh’d, Nana Firdausi, and Farida.
Kakakin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin.