
Donald Trump ya firgita Falasɗinawa kan shawarwarinsa game da makomar zirin Gaza, saboda ya ce Amurka za ta ƙwace iko da zirin tare sauya fasalinsa.
Wannan ne sauyi mafi girma game da manufofin Amurka kan yankin gabas ta tsakiya cikin gomman shekaru.
Trump ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a fadar White House tare da firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.
“Amurka za ta ƙarbi ikon zirin Gaza kuma za mu mallake zirin kuma mu dauki alhalin kwance nakiyoyin da aka dąsa sannan kuma gyara wuraren da aka lalata,” in ji Trump.
Nan da nan firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya nuna jin dadinsa ga kalaman na Mr Trump, inda ya ce hakan zai canza tarihi.
Netanyahu ya ce “ina kara maimaitawa, muradinmu uku ne kuma na uku shi ne tabbatar da cewa zirin Gaza bai kara zama barazana ga Isra’ila ba.”
Saudiyya ta mayar da martani cikin gaggawa kan ƙudurin Trump na shirin ƙwace iko da zirin Gaza, inda ta yi watsi da duk wani yunƙuri na raba Falasdinawa da ƙasarsu.
Saudiyyar ta ce ba za ta ƙulla wata alaƙa da Isra’ila ba har sai an samar da ƙasar Falasdinu.
Mai magana da yawun Hamas ya bayyana matakin da shirin haifar da hargitsi da rashin kwanciyar hankali a yankin.
Ƙasashen Masar da Jordan suma sun bayyana rashin amincewarsu da yunkurin na Trump na tsugunnar da Falasdinawa a ƙasashensu.
Shugaban Amurkar ya kuma bayyana abin da yake tunani game da makomar gabar yamma da kogin Jordan, inda ya ce yana tunanin nuna goyon bayansa ga shirin Isra’ila na kwace iko da gabar yamma din.
Netanyahu dai shi ne shugaban wata kasa na farko da ya kai ziyara fadar White House tun da Trump ya koma kan karagar mulki a karo na biyu.