Wednesday, October 9
Shadow

Masana’antar Kannywood Ta Samu Ƙaruwar Galleliyar Sabuwar Jaruma Daga Jihar Bauchi

Jarumar mai suna Sadiya Abdulƙadir wacce aka fi sani da (Sareena) sabuwar Jaruma ce duk da cewa ta ɗan kwana biyu a masana’antar ta Kannywood ana damawa da ita a fagen shirya fina-finan Hausa wadda ƴar asalin Jihar Bauchi ce ƙaramar hukumar Azare.

Fim na farko da ta fara yi tun bayan shigowarta masana’antar fim ne mai dogon zango mai suna (Aliya) wanda ake haska shi a (Youtube Channel) na Ali Jita, wato (Ali Jita Multimedia).

Yanzu haka dai Jarumar ta faso gada-gadan da zafinta domin cigaba da aikinta na faɗakarwa cikin fina-finan Hausa domin inganta tarbiyyar al’umma.

Photo Credit: Dk Photography

Wane fata zaku yi mata ?

Karanta Wannan  Idan 'yan kasuwa suka ki sayen man fetur dina zan fitar dashi kasar waje na sayar>>Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *