Thursday, October 3
Shadow

Motocin dake kan titunan Najeriya sun rage saboda tsadar rayuwa da wahalar man fetur

Babban lauya me rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana ya koka da cewa, tsadar rayuwa da wahalar man fetur yasa an sami karancin ababen hawa a titunan Najeriya.

Falana ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

Koken nasa na zuwane bayan da kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa bashi ya masa katutu wanda hakan zai iya shafar wadatar man fetur a Najeriya.

Falana yace a lokacin da rayuwa ke da sauki a Najeriya, kamfanin man na kasa,NNPCL ya bayyana cewa yana biyan kudin tallafin man fetur na lita miliyan 68.

Yace amma yanzu da aka shiga halin matsi, babu motoci da yawa akan titunan Najeriya, har yanzu dai NNPCL tana gayawa mutane cewa tana biyan kudin tallafi akan litar man fetur miliyan 68.

Karanta Wannan  DAMBARWAR MASARAUTAR KANO: Lauyoyin Sarki Aminu Ado Bayero Sun Janye Daga Tsaya Masa

Yace wannan ba abinda hankali zai dauka bane akwai wani abu da gwamnatin tarayya da kamfanin na NNPCL basa gayawa mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *