
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta rabawa ‘yan Najeriya kudin Tallafi har Naira Biliyan 300.
Gwamnatin tace ta raba wadannan kudade ne ga gidaje Miliyan 8.1.
Karamin Ministan Jin kai, Yusuf Sanunu ne ya bayyana hakan a Abuja a wajan wani taro da aka gudanar.
Yace hakan ya karfafa mutane ya inganta Iliminsu, ya kuma Inganta Lafiyarsu.
Hakanan yace akwai shirin baiwa wanda iftila’in Ambaliyar ruwa ta fadawa a fadin Najeriya tallafin Naira Biliyan 6.3 na bashi wanda babu ruwa.
Yace mutane 21,000 ne zasu amfana da wannan bashin.