Saturday, December 13
Shadow
Kalli Bidiyon yanda Magidanci ya hau saman katanga a Katsina yaki saukowa saboda bayan da surukansa suka je har gidansa suka tafi da matarsa

Kalli Bidiyon yanda Magidanci ya hau saman katanga a Katsina yaki saukowa saboda bayan da surukansa suka je har gidansa suka tafi da matarsa

Duk Labarai
Wani magidanci a jihar Katsina ya hau saman Katanga ya ki saukowa bayan da surukansa suka je gidansa suka dauko matarsa zuka tafi da ita. Yace ba zai sauko daga saman katangar ba sai an dawo masa da matarsa. Lamarin ya faru ne a Sabuwar Kofa, Katsina ranar Lahadi. Da farko dai an rika yada cewa barawone bayan da Bidiyon ya yadu sosai a Katsina. Amma daga baya kafar Katsina Daily News ta samo labarin ainahin abinda ya faru. Kalli Bidiyon anan
Matashiya ta aika kanta Lakhira saboda an tursasa mata auren abokin mahaifinta a jihar Borno

Matashiya ta aika kanta Lakhira saboda an tursasa mata auren abokin mahaifinta a jihar Borno

Duk Labarai
Wata matashiya a garin Gubio na jihar Borno ta Khashye kanta saboda mahaifinta ya tursasa mata sai ta auri abokinsa. Rahotan yace lamarin ya farune ranar lahadi da misalin karfe 6:20 na yamma. Matashiyar dai tana da wanda take so amma mahaifinta ya tursasa mata sai ta auri wanda bata so. Wani ma'aikacin sa kai a garin ya bayyana cewa lamarin ya jefa mutane cikin jimami.
Ji Farashin Dala a yau

Ji Farashin Dala a yau

Duk Labarai
Farashin da ake sayen dalar Amurka a yau, 20 ga watan October na shekarar 2025 shine Naira ₦1,468–₦1,475 a tsakanin bankuna. Daga CBN kuma ana sayenta akan Naira, ₦1,467.43 kan kowace dala. Sai kuma a kasuwar canji ana sayen dalar akan Naira ₦1,480 — Sell ₦1,500 
Kalli Bidiyon: Yanda Omoyele Sowore da sauran masu Zqngq-Zqngqr a saki Nnamdy Khanu a Abuja suke fece da gudu bayan da jami’an tsaro suka bhude musu whuta

Kalli Bidiyon: Yanda Omoyele Sowore da sauran masu Zqngq-Zqngqr a saki Nnamdy Khanu a Abuja suke fece da gudu bayan da jami’an tsaro suka bhude musu whuta

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, Dan Gwagwarmaya, Omoyele Sowore da sauran masu zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu sun fito zanga-zangar. Hakan ya kawo tsaikon ababen hawa sosai a Abujar. Tuni dai jami'an tsaro suka budewa masu zanga-zangar wuta wanda hakan yasa suka tsere ciki hadda shugaban zanga-zangar, Sowore wanda aka ganshi yana gudu. A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore yace 'yansandan sun kama Kanun Nnamdi Kanu da kuma Lauyansa sannan sun lakada musu duka. Yace suna neman a sake su nan take. https://twitter.com/YeleSowore/status/1980167258308841500?t=nkVhQT-0xbwX_Zee6L7W7Q&s=19 https://twitter.com/ArcSadam/status/1980172085583655235?t=576w70RrqZt4fHM2bAxnRg&s=19
Sanata Orji Uzor Kalu na neman a mayar da mulki shekara 6 wa’adi daya

Sanata Orji Uzor Kalu na neman a mayar da mulki shekara 6 wa’adi daya

Duk Labarai
Sanata Orji Uzor Kalu na neman a mayar da mulkin Najeriya na tsawon shekaru 6 amma wa'adi daya ga shugaban kasa da Gwamnoni. Ya jawo hankalin sanatoci 'yan uwansa dasu dauki wannan matsaya inda yace hakan zai baiwa shugaban kasa da Gwamnoni damar tsayawa su gudanar da mulki ba tare da neman zarcewa ya rika dauke musu hankali ba. Ya bayyana hakane a cikin wani Bidiyosa daya watsu sosai a kafafen sada zumunta. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1979971959090754026?t=Il_qxj0sVMj9CePn3WI-yA&s=19
Kalli Bidiyon: Ministan Kudi, Wale Edu  ya dawo Najeriya bayan jinya a kasar Waje

Kalli Bidiyon: Ministan Kudi, Wale Edu ya dawo Najeriya bayan jinya a kasar Waje

Duk Labarai
Ministan kudi, Wale Edun ya dawo gida Najeriya bayan jinyar da yayi a kasar Ingila. Wale Edun ya dawo Najeriya ne tare da tawagarsa. A baya dai an yada cewa Ministan ya kwanta rashin lafiya inda cutar shanyewar rabin jiki ta kamashi. Saidai daga baya Gwamnati ta musanta cewa ba cutar shanyewar rabin jiki bace ta kamashi amma dai da gaske bashi da lafiya.
Wani tsohon Gwamna ne daga kudancin Najeriya ake zargi da daukar Nauyin yiwa shugaba Tinubu juyin Mhulki, Ana shirin fara bincikensa

Wani tsohon Gwamna ne daga kudancin Najeriya ake zargi da daukar Nauyin yiwa shugaba Tinubu juyin Mhulki, Ana shirin fara bincikensa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Wani tsohon Gwamnane daga kudancin Najeriya ake zargi da hannu a shiryawa yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki. Rahotanni sun ce ana zargin Tsohon Gwamnan ne ya samar da kudaden da za'a gudanar da juyin mulkin kamar yanda gidan jaridar Daily Trust ta ruwaito. Rahoton yace har yanzu ana binciken alakar dakar tsakanin tsohon Gwamnan da sojojin da suka shirya juyin mulkin, kuma da zarar an samu tabbacin hannunsa, za'a gayyaceshi dan amsa tambayoyi. Rahoton yace ana kiyaye sunayen sojojin da suka shirya juyin mulkin dan kada a fitar dasu amma Daily Trust tace ta samu cewa akwai soja Brigadier general da kuma Captain. Tace kuma ana sojojin daya ya fito daga jihar Naija ne yayin da dayan ya fito daga jihar Nasarawa kuma yana da alaka da gida...
Masu shirin Yin Zqngq-Zqnzqr neman a Saki Nnqmd1 Kqnu sun ce ba gudu ba ja da baya duk da gargadin jami’an tsaro

Masu shirin Yin Zqngq-Zqnzqr neman a Saki Nnqmd1 Kqnu sun ce ba gudu ba ja da baya duk da gargadin jami’an tsaro

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, masu shirya zanga-zangar neman a saki shugaban Haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a yau Litinin, Sun ce ba gudu ba ja da baya duk da gargadin da jami'an tsaro suka musu. Masu zanga-zangar sun shirya yin tattaki zuwa fadar shugaban kasa dan neman a saki Nnamdi Kanu. Hakan kuma na zuwane a yayin da Babbar kotun gwamnatin tarayya ta hana masu zanga-zangar zuwa kusa da fadar gwamnati ko kuma kuma majalisar tarayya ko duk wani ginin gwamnati. Saidai duk da wannan, masu zanga-zangar sun ce ba gudu ba ja da baya, hakanan shugaban Zanga-zangar, Omoyele Sowore yace maganar umarnin Kotun ba gaskiya bane. Idan dai masu zanga-zangar suka fito, akwai yiyuwar za'a yi dauki ba dadi tsakaninsu da jami'an tsaro.