Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa Al'ummar Jihar sun taru inda aka sauke Qur'ani da kuma yiwa Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami Addu'ar Allah ya tsareshi daga sharrin EFCC.
Abubakar Malami dai yana tsare a hannun hukumar EFCC biyo bayan zargin da take masa na aikata ba daidai ba da kudaden kasa.
Tuni hukumar ta fara killace wasu kadarorinsa.
https://twitter.com/ADCVanguard_/status/2003206191288401976?t=lEPGJwFhRQF4LEFA7XVJBA&s=19
Rahotanni daga kasar Nijar na cewa, kasar ta Haramtawa 'yan kasar Amirka shiga kasarta da basu Visa.
Hakan na zuwane biyo bayan saka kasar Nijar cikin kasashen da Amirka ta haramtawa shiga kasarta.
Amirka ta saa hadda Najeriya da sauran wasu kasashe data kira Matalauta cikin kasashen data haramtawa shiga kasarta.
Hukumar jirgin kasa ta Najeriya, The Nigerian Railway Corporation ta sanar da rage farashin Tikitin jirgin da kaso 50 saboda bukukuwan karshen shekara.
Hukumar tace ragin zai fara aiki ne a yau, Talata.
A ranar 25 ga watan Disamba ne za'a yi bikin Kirsimeti sannan akwai bikin karshen shekara na 1 ga watan Janairu wanda duka Gwamnati ta bayar da hutu.
'Yan Kwallon kasar Misra/Egypt sun karanta Fatiha da suratul Ikhlas sau 3 a dakin canja kaya kamin wasansu da kasar Zimbabwe a ci gaba da gasar AFCON.
Bidiyon nasu ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda musamman musulmai suka rika musu fatan Nasara.
https://twitter.com/SalahUpdates/status/2003266206233755890?t=sRHJ59Q3V0Hiw2pwduOocA&s=19
Kuma sun yi nasara a wasan inda Egypt taci 2 Zimbabwe taci 1
Faston nan na kasar Ghana da ya ce wai an masa Wahayi Duniya zata tashi ranar Kirsimeti watau 25 ga watan Disamba kuma wai an ce masa ya kera jiragen ruwa 8 dan ya kwashi mutane a ciki saboda za'a yi ruwa irin na Dufana a yanzu ya fito yanawa mabiyansa bankwana.
Rahotanni sun ce wadanda suka yadda dashi tuni suka sayar da kadarorinsu suka koma wajansa da zama inda suke jiran ranar 25 ga wata tazo.
An ganshi ya fito yanawa mabiyan nasa bankwana.
https://twitter.com/OzorNdiOzor/status/2003172382266290185?t=OmsYRbBH1RqQiyr_YeBMRQ&s=19
Kasar Amurka ta sanar da cewa, duk dan Chiranin dake kasar ta amince zata bashi dala $3000 kwatankwacin sama da Naira Miliyan 4.3 kenan idan ya yadda ya koma kasarsa.
Kasar ta bayyana hakane daga Ma'ikatar DHC inda a baya dala $1000 ce kawai ake baiwa 'yan Chiranin idan sun amince zasu koma kasashen nasu.
Hukumar tace daga watan Janairu na shekarar 2025 zuwa yanzu 'yan Chirani akalla Miliyan 1.9 suka amince su koma kasashen su daga kasar Amirkar ba tare da an kamasu ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka tace ta janye matakin soji da take son dauka akan Najeriya bisa zargin Kisan Kiristoci.
Tace a yanzu bayan ta fahimci yanda abin yake ta gane abune da za'a iya warwareshi ta hanyar diplomasiyya.
Amurkar ta canja matsayine bayan ganawar 'yan majalisar kasar, Bill Huizenga da Reps. Michael Baumgartner, Keith Self, da Jefferson Shreve, babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu.
Tace ta fahimci akwai banbancin rikicin dake faruwa a Arewa maso gabas da Arewa maso tsakiya.
Tace amma zata ci gaba da aiki da Najeriya wajan ganin lamuran tsaro sun inganta.
An ga wani sabon Bidiyon Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Kinal da Angonta suna rungumar juna wanda matar Rarara, Aishatulhumaira ta wallafa da yammacin yau.
Hakan na zuwane bayan da aka daura aurensu.
Da yawa sun yi ta sam barka kan lamarin.
https://www.tiktok.com/@aishatulhumairah/video/7586772365858573579?_t=ZS-92RZuiHFtyL&_r=1
Matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta bayyana cewa, an so a fitar da ita daga fadar shugaban kasa lokacin mijinta na mulki amma taki yadda.
Tace wani jami'in tsaro ya ce mata ya kamata ta koma Daura da zama saboda suna son yin wani bincike idan an kammala sai ta dawo.
Saidai tace amma taki amincewa da hakan.
A'isha Kuma a cikin Littafin tarihin Rayuwar Buhari da aka rubuta tace babbar matsalar mijin nata yasan bara gurbi a gwamnatinsa amma yaki ciresu daga mukaminsu.
Tace tana fatan Shugaba Tinubu ba zai tafka irin kuskuren da mijin nata a tafka ba.