Wannana wata Amarya ce da aka mata gyaran da ya dauki hankula kamar ba ita ba.
https://www.tiktok.com/@samrahtouch/video/7583673232297872660?_t=ZS-92FP2rS1JuS&_r=1
Wani malamin Dariqa ya bayyana inda yake cewa, Sheikh Tijjani ya baiwa kowane dan Darika Aljannah.
Yace abinda ya ragewa mutane shine su ma su yi aikin da zasu ceto wasu.
https://www.tiktok.com/@aliyu.muhammad845/video/7584081756316372280?_t=ZS-92FOTwW1Af3&_r=1
Taurarin fina-finan Hausa Mata, sun kai tallafin kayan abinci gidan marayu.
Wadanda aka gani a wajan sune Momi Gombe, Samha M. Inuwa, Amal Umar da sauransu.
An ga sun kai buhunan shikafa da madara da sauransu.
https://www.tiktok.com/@realmahrazhamraz/video/7583770200386964744?_t=ZS-92FNOZn68en&_r=1
Fasto Chris Okafor wanda Inyamuri ne ya bayyana cewa su Inyamurai halayensu basu da kyau.
Yace Hausawa na girmama na gaba dasu, Yarbawa ma na girmama na gaba dasu amma banda Inyamurai.
Yace Inyamuri shi kudinshi ne a gabanshi.
https://twitter.com/kepukepunews/status/2000484512946597894?t=gfLTdrf1FY0DreRkXVQ3sQ&s=19
Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya bayyana cewa, masu shigo da man fetur daga kasashen waje duk da matatarsa dake aiki ba zai hanasu ba.
Yace su ci gaba.
Yace amma suna da motocin Dakon mai gida 4000 da ya siyo kwanakin baya, kuma yace idan ma basu isa ba, zai sake siyo wasu.
https://twitter.com/NigeriaStories/status/2000500235114631639?t=JwrC2h48JYnkvlH9aX6Aeg&s=19
Me kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu BUA ya bayyana cewa, IMinista Hannatu Musa Musawa tsohuwar matarsa ce.
Ya bayyana hakane a wajan taron nasarorin daya samu a kamfaninsa sannan kuma bayan hakan sun rungumi juna inda suka dauki hotuna tare.
https://twitter.com/gamawa_amina/status/2000511064929153206?t=_9aQptNsQ_zjFdwCXwUhNg&s=19
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya halarci wajan taron kaddamar da littafin da aka rubuta akan rayuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
An yi taronne a babban dakin taron dake fadar shugaban kasar.
Sannan kuma Littafin ya hakaito muhimman abubuwan da suka faru a rayuwar tsohon shugaban kasar.
https://twitter.com/BashirAhmaad/status/2000538541865029721?t=zIBi5arjFyhyA9hhob4E2g&s=19
https://twitter.com/DOlusegun/status/2000565336064582048?t=SyE87vzJy_XGrW85z4dDXQ&s=19
https://twitter.com/NTANewsNow/status/2000580575799742687?t=ppsiGtAvAgCLLgrtqucg7w&s=19
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami ya bayyana cewa, bai yadda da shugaban EFCC ba saboda ba zai masa Adalci ba.
Malami ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Muhammad Doka.
Inda yace a lokacin yana ministan shari'a, Kotu ta bayar da umarnin yin bincike kan wani zargin aikaa ba daidai ba a EFCC wanda kuma a wanca lokacin shi shugaban EFCC na Yanzu, Mohammad Doka shine sakataren Hukumar.
Yace dan haka yanzu abubuwa da yake masa kamar ramuwa ne da bita da kulli da ya koma ADC.
Yace dan aka yake neman a cireshi daga mukamin.
Hukumar kula da kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa, farashin kayan masarufi ya sauka sosai.
Hukumar ta bayyana hakane a cikin bayanan watan Nuwamba da ta fitar ranar Litinin a shafinta.
Tace idan ak kwatanta da shekarar data gabata, alkaluman farashin kayan Masarufin na kan maki 16.05 wanda kuma a yanzu suna kan makin 14.45.