Jimullar ‘yan Najeriya 55,910 ne aka kashe an kuma yi garkuwa da 20,000
Wata kungiya dake saka ido akan harkokin tsaro ORFA ta bayyana cewa daga shekarar 2019 zuwa 2023 an samu kashe mutane 55,910 da yin garkuwa da guda 20,000.
Kungiyar tace kungiyoyin IS-WA-P da B0k0 Haram ne da takwarorinsu suka yi wadannan aika-aika.
A ranar Alhamis ne kungiyar ta fitar da wannan bayani inda tace amma kiristoci ne suka fi fuskantar wannan matsala.
Wakilin Kungiyar, Frans Vierhout ya bayyana cewa hakan ya nuna yanda lamuran tsaro suka tabarbare a Najeriya.