Gyaran gashi da ruwan shinkafa
Mutanen kasar China da Japan sun dade suna amfani da ruwan shinkafa wajan kara tsawon gashi da kuma hanashi yin furfura.
Hakanan kuma a wani kaulin,ruwan Shinkafa na hana gashin mumurdewa da hadewa da juna.
Hakanan kuma ruwan shinkafa na karawa gashin kai sheki.
Matan wani kauye a China me suna, Huangluo na daga matan da suka fi kowane mata tsawon gashi a Duniya inda aka ruwaito cewa gashin kansu hana kai tsawon kafa 6.
Sannan kuma gashin kansu yawanci bai fara yin furfura sai sun kai kusa da shekaru 80 a Duniya.
Wadannan mata sun bayyana cewa sirrinsu shine wanke gashin kansu da suke yi da ruwan shinkafa.
YANDA ZA'A SAMU RUWAN SHINKAFA DAN GYARAN GASHI
Akwai hanyoyi 3 da ake samun ruwan shinkafa dan gyara gashi dashi.
Danyar Shinkafa: Ana samun danyar Shinkafa rab...