Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya lamarin na damunshi.
Ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a wayar da kawunan mutane game da hakan.
Shugaban ya bayyana hakane bayan kammala sallar Idi a jiya, Lahadi.
Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yanda mutane da yawa suka rungumi harkar Noma.
Shugaban yace nasarar kasa ta dogara ne akan zamun shuwagabanni masu nasara akai-akai.