Tuesday, December 16
Shadow
Kotu ta aikawa bangaren su David Mark sammace akan shugabancin jam’iyyar ADC

Kotu ta aikawa bangaren su David Mark sammace akan shugabancin jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta aikawa shugaban jam'iyyar ADC na riko, David Mark takardar sammace inda tace ya je ya kare kansa akan shugabancin jam'iyyar. Motun ta bukaci David Mark da sakataren riko na jam'iyyar ADC, Rauf Aregbesola su je su gaya mata dalilan da zasu hana a tsigesu daga shugabancin jam'iyyar. Hakan na zuwane bayan da Nafiu Gombe ya gabatar da kara a kotun inda yake cewa shine halastaccen shugaban jam'iyyar ADC ba David Mark ba. Ya kuma bukaci kotun data tsige David Mark daga shugabancin jam'iyyar ADC. Saidai kotun bata amsa bukatarsa ba inda tace maimakon tsige David Mark, tana bukatar ya bayyana a gabanta kamin 15 ga watan Satumba dan ya bata hujjojin da zasu sa kada a tsigeshi daga shugabancin jam'iyyar ADC.
Malamai sun sauke Qur’ani a Kano dan nasarar Shugaba Tinubu a 2027 da kuma takarar Gwamna ta Sanata Barau Jibrin

Malamai sun sauke Qur’ani a Kano dan nasarar Shugaba Tinubu a 2027 da kuma takarar Gwamna ta Sanata Barau Jibrin

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an gudanar da addu' da yankan Dabbobi sannan an sauke Qur'ani saboda neman Allah ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau Jibrin Maliya nasara a 2027. Rahoton yace an yi wanan taronne a gidan Baballiya dake Kurna karamar hukumar Fagge dake Kano. Kuma mutane daga kowacce karamar hukumar a jihar sun samu halarta. Bayan kammala saukar Qur'anin, an gabatar da addu'a ga Shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau Maliya kan Allah ya basu nasara. Sannan kuma malaman sun yi Addu'ar Allah ya bada zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki a Najeriya baki daya.
Kalli Bidiyo: Anata ta rububin daukar hotuna yayin da wai Gibirima ya bayana a bango a Najeriya yayin Maulidi

Kalli Bidiyo: Anata ta rububin daukar hotuna yayin da wai Gibirima ya bayana a bango a Najeriya yayin Maulidi

Duk Labarai
Wannan wani Bidiyo ne inda aka ga mutane nata rububin daukar hotuna yayin da aka ce Gibirima ya bayyana a bangon wani gini. Hakan ya farune yayin bikin Maulidi da ya gabata. https://www.tiktok.com/@kingyahay1/video/7547072216781819153?_t=ZS-8zf0tEIWDeD&_r=1 A baya dai an rika cewa Inyas ko sauran shehunai na darika sun bayyana a jikin bango.
Hada Fim da Waka da Addini, Izgiline, ba zasu taba haduwa ba har Duniya ta nade>>Inji Me wakar Baatsq, Soja Boy

Hada Fim da Waka da Addini, Izgiline, ba zasu taba haduwa ba har Duniya ta nade>>Inji Me wakar Baatsq, Soja Boy

Duk Labarai
Tauraron me wakar Batsa wanda ya fito daga jihar Sokoto, wanda aka fi sani da Soja Boy ya bayyana cewa hada addini da harkar Nishadi ko rawa da waka Izgili ne. Ya bayyana cewa Addini da rawa da fim da waka ba zasu taba haduwa ba har abada. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. https://www.tiktok.com/@usmansuleyman2/video/7546990774999682312?_t=ZS-8zezVeYgAaH&_r=1 Soja Boy dai yana shan suka sosai a wajan mutane musamman ma kwanannan shine yayi waka da matashiyar 'yar Fim iftihal Madaki wadda aka saba ganinta da Hijabi amma rana daya aka ganta tana rawa da mawaka.
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Saheer Abdul ya fashe da kuka saboda irin mata ke aika masa ya taya su addu’ar neman mijin aure da kuma neman zaman lafiya da mazajensu

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Saheer Abdul ya fashe da kuka saboda irin mata ke aika masa ya taya su addu’ar neman mijin aure da kuma neman zaman lafiya da mazajensu

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Saheer Abdul da ya je Madina, ibada da sayar da garin Danwake yace da yawan wadanda ke aika masa da neman ya taya su da addu'a matane. Yace kuma yawanci suna cewa ne ya nema musu addu'ar Allah ya basu mazajen aure wasu kuma suna kiran ya taya su da addu'ar Allah yasa su samu zaman lafiya da mazansu. Yace irin labaran da matan ke bashi akwai ban tausai. Ya sha Alwashin taya su da addu'a. https://www.tiktok.com/@mr_saheeer/video/7548756716633066760?_t=ZS-8zeyAXIqm5w&_r=1
Ji Labarin yanda aka yaudari wata matashiyar Najeriya aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket amma aka ce Qaruwanciy zata yi

Ji Labarin yanda aka yaudari wata matashiyar Najeriya aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket amma aka ce Qaruwanciy zata yi

Duk Labarai
Wata matashiyar Najeriya me suna Faith Joseph ta ki amincewa da yin karuwanci bayan da aka yaudareta aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket. Matashiyar na aikin gida ne a Afuze, Owan East dake jihar Edo inda aka ce za'a kaita Legas dan ta yi aiki a Supermarket. Saidai daga baya an tafi da ita kasar Mali, tace sina zuwa aka kaita wajan wata mata wadda Magajiyace, watau uwar Karuwai, data lura da haka sai tace bata yadda ba, ba zata yi ba. Saidai magajiyar ta gaya mata cewa, aikuwa saidai idan an kawo wata da zata maye gurbinta ne sannan zata iya komawa gida Najeriya. Matashiya, Faith haka ta zauna har Allah yasa ta lura da wani Ofishin 'yansanda inda ta tsere zuwa can. Daga baya dai ta samu an dawo da ita zuwa gida Najeriya. Shugaban hukumar kula da 'y...
Da Duminsa: An samu Matuka jirgin saman Air Peace da shaye-shayen abubuwan Maaye

Da Duminsa: An samu Matuka jirgin saman Air Peace da shaye-shayen abubuwan Maaye

Duk Labarai
Rahotanni daga hukumar bincike ta kasa, The Nigerian Safety Investigation Bureau sun bayyana cewa, an samu biyu daga cikin matuka jirgin saman kamfanin Air Peace da shaye-shayen miyagun kwayoyi. Abubuwan da aka samesu da sha shine kwayoyi da kuma giya. Hakan na zuwane bayan da jirgin da suke tukawa ya kaucewa hanya a filin jirgin samana na Fatakwal a ranar July 13, 2025. Me magana da yawun hukumar binciken ta Najeriya, Mrs Bimbo Olawumi Oladeji ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai na jaridar Punchng. An gano cewa matuka jirgin sun yi wasa da rayuwar mutane 103 da suke dauke dasu a wancan lokacin.
Jihar Delta ta yi dokar hana Ma’aikatan jihar Tara gemu da yawa

Jihar Delta ta yi dokar hana Ma’aikatan jihar Tara gemu da yawa

Duk Labarai
Jihar Delta ta yi sabuwar doka game da irin kayan da ya kamata ma'aikatan jihar maza da mata su rika sakawa. A wata sanarwa data fitar a yau, Alhamis, Jihar tace dolene ma'aikata su rika saka kayan mutunci a yayin da suka je wajan aiki. Sanarwar tace ana tsammanin maza su rika saka kwat ko riga 'yar ciki su tsuke in banda ranar Juma'a da zasu iya saka kayan gida. Hakanan ba'a so mutum ya tara gemu da yawa ba aski, ba gyara. Mata kuma su saka siket wanda zai rika wuce gwiwarsu.