Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a shekara daya da ta yi tana mulki, ko me aka yi da kudin?
Masana sun bayyana damuwa game da yawan bashin da gwamnatin tarayya ta ciwo a shekara daya data gabata.
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a hannun 'yan Najeriya.
Hakan na nuna cewa, yawan bashin da gwamnatin Tinubu ta ciwo ya fi wanda Gwamnatin Buhari ta ciwo a shekararta ta karshe akan mulki da kaso 117.
Masana sun bayyana damuwar cewa hakan zai iya kawo karuwar hauhawar farashin kayan abinci da kara kudin ruwa na karbar bashi.