Monday, December 15
Shadow

Ji abin mamaki ga rayuwar dan daba daya addabi Kaduna, Watau Habu dan Damusa da aka kashe

Duk Labarai
Habu dan Damusa da ya rigamu gidan gaskiya ya gamu da ajalinsa ne a hannun jami'an tsaro kamar yanda rahotanni suka bayyana. Wasu sun rika murna da mutuwarsa inda wasu kuma suka rika jimami da nema masa rahama. Saidai sabon bayani da ya fito game dashi shine, ashe gadon daba yayi, mahaifinsa ma dan dabane, kuma shima an kasheshi ne ranar da aka haifi Habu Dan Damusa. Hakanan ga habu shima an kasheshi kwana daya bayan da aka haifa masa diyarsa. https://twitter.com/Sarki_sultan/status/1960989309206466569?t=cNfVTM0kI8AqjUnrJ_cgQg&s=19
Kalli Bidiyo: ‘Yan darika an kunyata, An yi rawar Maulidi, Maulidi bashi da tushe a addini>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Kalli Bidiyo: ‘Yan darika an kunyata, An yi rawar Maulidi, Maulidi bashi da tushe a addini>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa, 'yan Darika sun ji kunya, Sun yi rawa a wajan Maulidi. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da aka ganshi yana wa'azi. Malam ya nanata cewa, Maulidi bashi da Asali a addini. https://www.tiktok.com/@i_am_saeed01/video/7543574023129615622?_t=ZS-8zHMj7MJAuX&_r=1
Karanta Jadawalin kasuwanci guda 17 da Dangote ke yi

Karanta Jadawalin kasuwanci guda 17 da Dangote ke yi

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote na da kasuwanci kala 17. Ga jerinsu kamar haka: Automotive - Kayan MotociCement manufacturing - SimintiEnergy - MakamashiFertilizer - Takin ZamaniLogistics - Kayan amfanin yau da kullu Infrastructure - Raya kasaMaritime - Sufurin TekuMining - Hakar ma'adanaiPetrochemicals - Matatar maiPolysacksReal Estate - Harkar GidajeRefineryRice farming - Noman Shinkafa Salt & seasoning - Gishiri da MagiSugar refining - SukariTomato farming - TimatiriTraining academy - Makaranta.
Na ji dadin Dawowa Najeriya, Kuma ina gina sabuwar Najeriya fil>>Shugaba Tinubu

Na ji dadin Dawowa Najeriya, Kuma ina gina sabuwar Najeriya fil>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya ji dadin dawowa Najeriya daga ziyarar da ya kai kasashen Japan da Brazil. Shugaba Tinubu ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace daya daga cikin aikin da 'yan Najeriya suka bashi a shekarar 2023 shine na kulla hadaka da kasashen Duniya dan kawo ci gaba. Shugaban yace a ziyarar da ya kai kasashen Brazil da Japan Najeriya ta kulla yarjejeniya da kasashen a fannonin kudi, sufuri, kimiyya da fasaha da sauransu.
Da Duminsa: Ina cikin tsama mai wuya, ana barazanar rabani da kujerara>>Inji Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari

Da Duminsa: Ina cikin tsama mai wuya, ana barazanar rabani da kujerara>>Inji Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari

Duk Labarai
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ya bayyana cewa, Rayuwarsa data sauran ma'aikatan kamfanin na cikin hadari. Yace ana barazanar saukeshi daga kan mukaminsa, inda yace laifinsa kawai shine kyaran da ya kawo a harkar mai a kasarnan kamar yanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bashi umarni. Ya bayyana hakane a Abuja yayin da kungiyar ma'aikatan man, PENGASSAN ta kai masa ziyara bisa jagorancin shugabanta, Comrade Festus Osifo. Yace suna kokarin ganin an gyara matatun man fetur din Najeriya sun dawo aiki yanda ya kamata.
Matar Gwamnan jihar Borno ta karrama ma’aikataciya me daukar albashin Naira 30,000 data mayar da Naira Miliyan 4.8 da aka tura mata bisa kuskure kyautar Naira miliyan 1

Matar Gwamnan jihar Borno ta karrama ma’aikataciya me daukar albashin Naira 30,000 data mayar da Naira Miliyan 4.8 da aka tura mata bisa kuskure kyautar Naira miliyan 1

Duk Labarai
Matar gwamnan jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Zulum ta karrama Faiza Abdullahi wadda karamar ma'aikaciyace dake daukar Albashin Naira dubu 30 bayan da ta mayar da Naira Miliyan 4.8 ds aka tura mata bisa kuskure. Hakanan matar gwamnan ta bata kayan abinci da sauran kyautuka. Faiza dake aiki a jami'ar Maiduguri, UNIMAID ta bayyana cewa ta mayar da kudin da aka tura mata ne saboda tsoron Allah.
Kotu ta daure shahararren me zakkewa matan mutane a kasar Guinea daurin shekaru 8 a gidan yari

Kotu ta daure shahararren me zakkewa matan mutane a kasar Guinea daurin shekaru 8 a gidan yari

Duk Labarai
Kotu a kasar Guinea ta daure Baltasar Engonga durin shekaru 8 a gidan yari. An sameshi da zargin zakewa matan mutane da kuma almun dahana. A baya dai ab ga Bidiyonsa inda yake lalata da matan mutane daban-daban a ofis dinsa da gurare daban-daban. Saidai wasu rahotanni sun ce an masa wannan tonin silili ne saboda yunkirin da yayi na tsayawa takarar siyasa.
Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027, ba zan janyewa kowa ba>>Inji Rotimi Amaechi

Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027, ba zan janyewa kowa ba>>Inji Rotimi Amaechi

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, kuma jigo a jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi ya ce babu-gudu-ba-ja-da-baya a kan takarar shugaban kasa da yake son yi a 2027. A wata hira da ya yi da manema labarai a Kano, Amaechi wanda kuma ya kasance ministan sufuri na kasar daga 2015 zuwa 2022, a lokacin gwamnatin Buhari, ya ce babu batun yin sulhu idan aka zo zaben fid da gwani a jam'iyyar ADC. Ya tabbatar da cewa kowa yana da damar fitowa takarar shugaban kasa kamar yadda tsarin jam'iyyar ya nuna. Amaechi ya bayyana haka ne yayin wani taro da hadaddiyar kungiyar 'yan kasuwar jihar Kano da suka gayyace shi, inda ya ce abu ne mai kyau kowa ma ya fito takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC in ya so tasa ta fissheshi. Tsohon gwamnan na Rivers, ya ce akwai kyakkyawar d...
Goodluck Jonathan na son a sauya yadda ake zaɓen shugaban INEC

Goodluck Jonathan na son a sauya yadda ake zaɓen shugaban INEC

Duk Labarai
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kira da a samar da sabon tsarin zaɓen shugaban hukumar zabe ta ƙasa (INEC), inda ya ba da shawarar kafa wani tsarin tantancewa da zaɓe mai zaman kansa don ƙara wa hukumar sahihanci kafin zaɓen gaba na 2027. Jonathan ya bayyana wannan ra’ayi ne a ranar Laraba a Abuja, a yayin gabatar da shirin ƙasa na gyaran harkokin zaɓe, wanda Makarantar Nazarin Zamantakewa da Siyasa ta Abuja ta shirya. Kiran ya zo ne a wani lokaci na siyasa mai ɗaukar hankali, yayin da wa’adin shugaban INEC na yanzu, Prof. Mahmood Yakubu, ke ƙarewa a watan Oktoba na wannan shekara. Yakubu, wanda ya jagoranci zaɓukan 2019 da 2023, ya riga ya yi wa’adin aiki biyu, kuma zaɓen wanda zai gaje shi na janyo ƙarin hasashe a al’umma. Masana na ganin cewa wanda zai zam...
Ba na so na tsaya takara a 2027 – El-Rufai

Ba na so na tsaya takara a 2027 – El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba ya tunanin tsayawa takara a zaɓen ƙasar na shekara ta 2027 ba. Ya ce dawowarsa harkar siyasa kwanan nan "ba don neman muƙami ba ne, sai don tallafa wa shugabanci nagari a dukkan matakai". El-Rufai ya yi wannan bayani ne yayin wani taron siyasa a jihar Kaduna ranar Laraba. "Asalin shirina bayan barin gwamna a 2023 shi ne na huta daga siyasa, amma abubuwan da suka faru kwanan nan ne suka tilasta min dawowa, ba don kaina ba, amma domin na bayar da goyon baya," in ji El-Rufai. El-Rufa'i ya ce "ni dai ba zan sake yin gwamna ba, ba na so na je senate (Majalisar Dattijai), ba na wata takara". Ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu, inda ya ce ta gaza. Nasir El-Rufa'i na cikin manyan ƴan...